Matuƙin Keke Napep ya mayar da miliyan 15 da wani fasinja ya manta a mashin ɗinsa

Wani matashi ɗan shekara 22 mai suna Auwalu Salisu ya mayar da Naira miliyan 15 da wani fasinja da ya zo daga ƙasar Chadi sayo kaya a Kano ya manta a mashin ɗinsa.

Salisu ya mayar da kuɗin ne bayan an sanar da ɓacewarsu a wani gidan rediyo a Kano, PM News.

Ya shaida wa gidan rediyon cewa bai lura fasinjan nasa ya manta da kuɗin ba har ya isa gida.

Ya ce bayan gano kuɗin ne ya sanar da iyayensa waɗanda suka umarce shi da ya je ya nemo mai shi.

“Na ɗauki mutumin daga Badawa zuwa Bata.  Na koma can bayan sanar da iyayena.  Lokacin da na isa wurin, ban same shi ba kuma na ci gaba da bincike.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta mayar wa wata mata miliyan 19 da gida da mota

“Na koma gida na ba mahaifiyata kuɗin da ta ajiye a cikin tufafinta.  Na ji tsoro domin ina ɗokin mayar da kuɗin ga mai shi.  Ba ni da niyyar taɓa ko kwabo.  ba nawa ba ne, kamar yadda aka haramta mani, ”in ji shi.

Yayin da shi da iyayensa ke tunanin mafita, sai ya ji sanarwa a rediyo, aka ba da lambar mai kuɗin.

“Na ji sanarwar a gidan rediyon Arewa, kuma sun ba da lamba.  Na ƙira lambar sai mai kuɗin ya ce zai zo gidanmu, amma na ce a’a.  Mu haɗu a Gidan Rediyo.  Mun haɗu a can na ba shi kuɗinsa”.

Salisu wanda ya samu rakiyar iyayensa ya ce ba shi da niyyar taɓa kuɗin duk da halin da suke ciki a gida.

“Da ƙyar muke yin girki sau biyu a rana, ko jiya ba ma iya yin girki yayin da kuɗin ke tare da mu,” in ji mahaifinsa.

A nasa ɓangaren, mai kuɗin ya ce bai taɓa tunanin akwai mutanen kirki irin wannan yaron a duniya ba. 

Da yake magana ta bakin ɗan uwansa Musa Hassan, mai gidan ya yabawa yaron da iyayensa da suka rene shi yadda ya kamata.

“Ban taɓa tunanin akwai irin waɗannan samarin a duniya ba. Alhamdulillah!  Ina matuƙar godiya da shi da iyayensa.  Suna fuskantar matsaloli amma ba su taɓa ko kwabo daga cikin kuɗinsu ba, ”in ji mai gidan.

A ƙarshe mutumin ya baiwa matashin tallafin tukuicin Naira dubu ɗari huɗu (400,000) domin nuna godiyarsa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *