Daga Wakilinmu
Matsalar tsaro na ci gaba da tada hankula da daidaita al’umomi a yankunan arewacin Najeriya, baya ga mutanen da ke rasa rayuka ana kuma samun karin mutanen da ke gudun hijira.
Harin baya-bayanan da ya daidaita mutane da gidajensu shi ne wanda aka kai garuruwan Zamfara da Katsina a cikin wannan makon.
Ko a maraicen jiya Talata sai da ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Hayin Dan Maciji na yankin karamar hukumar Gusau a Zamfara tare da hallaka mutane.
Sai dai yayin da ake cikin wannan yanayi su kuwa jama’ar garin garin Doma na jihar Katsina jajircewa suka yi, suka fatattaki wasu ‘yan bindiga da suka yi yunkurin kai masu hari.
Zuwa wayewar safiyar wannan Larabar mafi rinjayen jama’ar garin Hayin Dan Maciji na gundumar Ruwan Baure a yankin karamar hukumar Gusau, sun tsere zuwa wasu garuruwa makwabta.
Wani mutumin garin, wanda muka zanta da shi a kan hanyarsa ta gudun hijira, ya shaidawa BBC irin halin tashin hankalin da suka shiga:
”Muna cikin mawuyacin hali, da mu da iyalan mu da yara duk mun tarwatse, wasu ma ba su san inda ‘yan uwa da abokan arzikinsu suke ba.
Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus
Maharan sun kawo hari muna tsaka da sallar la’asar, su ka zo da manyan makamai, sun saba shigo mana amma wannan karon harbin mutane kawai suka dinga yi, kowa suka samu harba suke yi, wanda ya tsere to ya kuɓuta.
Kuma an ce su na can garin sun ja daga lamarin ya sha kanmu, ba mu san yadda za mu yi ba.”
Ita ma wata mata, mai ɗanyen goyo wadda ta gudu ta bar sauran ‘ya’yanta a garin na Hayin Dan Maciji, ta yi wa Wakilinmu karin bayani a kan hanyarta ta tserewa zuwa garin Kwatarkwashi.
Ta ce: ”To ni yanzu gani nan dai ban san abin da ake ciki ba, na baro gida babu shiri, kuma can na baro ‘ya’yana biyar ban san halin da suke ciki ba.
Da ta goye kawai na gudo, anan tare dani akwai mata sun kai goma da muka yo gudun hijira, mu na hanyar tafiya Kwatarkwashi, kuma da kafa muka yi tafiyar nan ta kusan mil ashirin, ba mu dauko komai ba.”
An kashe mutane da dama amma ban san adadinsu ba, sai dai an kai wasu da yawa asibiti, mu na cikin mawuyacin hali,” in ji matar da ba ta so a ambaci sunan ta ba.
To yayin da ake cikin wannan yanayi can a garin Doma na yankin karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina, jama’a ne suka yi kukan kura, suka tunkari ‘yan bindigar da suka yi yunkurin kai masu hari a ranar Lahadin da ta gabata.
Wani mazaunin garin ya ce sun gaji da abin da ‘yan bindigar ke yi musu na kai hari ba gaira ba dalili, don haka suka dauki matakin rarakarsu.
”Sun yi kokarin su shiga gari Allah ya hana, matasa suka jajirce suka hana, ba mu da makamai sai adda da barandami, mu ka rarakesu, har bayan gari sun kashe mana mutum 10 da wasu 11 rauni, ba ma tsoron su sake dawowa mun dogara da Allah, jami’am tsaro mun kira su amma ba su zo ba sai kawai muka dauki matakin kare kan mu.”
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin SP Muhammad Shehu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Zamfara, da takwaran aikinsa SP Gambo Isa na jihar Katsina, kuma dukkansu sun ce za su bincika su kira mu.
Amma har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto ba mu ji daga gare su ba.
Jihohin Zamfara da Katsina na daga cikin wadanda ke fama da matsalar tsaro a arewacin Najeriya, inda ‘yan bindiga ke kai hare-hare da kashe mutane, da satar dabbobi da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Al’ummar garuruwan jihohin na ci gaba da fuskantar matsaloli da yin gudun hijira suna barin dukiyoyinsu, ya yin da wasu rahotanni ke cewa ‘yan bindiga na dorawa mutanen haraji matukar su na son zaman lafiya.