Matsalar Ruwa Sha: Yaushe dokar ta-ɓacin Gwamnatin Kano za ta fara aiki? ‎

0
210
Matsalar Ruwa Sha: Yaushe dokar ta-ɓacin Gwamnatin Kano za ta fara aiki? ‎

Matsalar Ruwa Sha: Yaushe dokar ta-ɓacin Gwamnatin Kano za ta fara aiki? ‎

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Jihar Kano na fuskantar matsalar ruwa mai tsanani, musamman a lokutan zafi da suke kara tsananta yanayin rayuwa ga mazauna jihar.

Al’ummar yankuna daban-daban na kokawa kan yadda suke shan wahala wajen samun ruwan amfanin yau da kullum.

‎Rahotanni daga jaridar Neptune Prime sun bayyana cewa matsalar ta fi shafar mazauna kananan hukumomi takwas da ke cikin kwaryar birnin Kano, wadanda suka hadar da karamar hukumar Dala, Fagge, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Tarauni, Nassarawa, da kuma karamar hukumar Ungogo.

Wadannan yankuna sun dogara ne kan samar da ruwa daga ma’aikatar ruwa ta jiha, rijiyoyin burtsatse da gwamnati ko masu hannu da shuni ke samarwa, da kuma tallafin ‘yan garuwa masu sayar da ruwa.

A yankunan karkara kuwa, matsalar ta fi kamari inda jama’a ke fama da matsanancin rashin tsaftataccen ruwan sha, matsalar da ta jima tana addabar su fiye da shekaru hamsin.

KU KUMA KARANTA:Matsalar ruwan sha, Gwamnatin Kano za ta kai ɗauki a Warawa – Kwamishinan Muhalli

A wasu lokuta, ana kwana a wuraren neman ruwa, wanda sau da yawa ba shi da tsafta. Wani mazaunin yankin Mai suna Malam Balarabe ya bayyana cewa “Ruwan da dabbobi ke wanka a ciki, mu ke amfani da shi don sha da sauran bukatu.”

A wasu kauyuka, mutane da jakuna na amfani da ruwa daya, lamarin da ke jefa rayuwar mutane cikin hadarin kamuwa da cututtuka.

‎Bincike ya nuna cewa ana danganta matsalar ruwan da gazawar tsarin wutar lantarki, wanda ke haddasa cikas ga aikin bututun ruwa, ko kuma rashin kayan aiki a cibiyoyin sarrafa ruwa. Wannan matsala ta kara tsananta wahalar da al’ummar jihar ke fuskanta.

‎A kokarinsa na magance matsalar, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ayyana dokar ta-baci a bangaren samar da ruwa domin kawo karshen wahalar da al’umma ke fuskanta. Sai dai har yanzu, jama’a na ci gaba da tambaya: Yaushe wannan dokar zata fara aiki? Kuma shin zata kawo karshen matsalar ruwan da ake fama da ita a jihar?

‎Dole ne a dauki matakan gaggawa domin tabbatar da cewa wannan dokar ta-baci ba ta tsaya a takarda ba kawai , sai an aiwatar da ita ta yadda al’ummar Kano za su samu saukin wahalar ruwan da ta addabe su shekaru da dama.

Leave a Reply