Matar Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da shirin biyan bashi a mutane 1,000 dake tsare a gidan gyaran hali
Daga Idris Umar, Zariya
Hajiya Huriyya Dauda Lawal tare da haɗin gwuiwa da Hukumar Zakka da waƙafi, ta biya wa mutane dubu ɗaya da a kebin su basussuka da ke tsare a gidan gyara hali da wajan hukumomi da masarautu goma shatara da ke cikin jihar tare da bayar da tallafin shinkafa da kuɗi ga marasa galihu domin taimakawa wajen rage raɗaɗin talauci da ake fama da shi a cikin jihar.
Babbar Mataimakiya ta musamman ta Uwar gidan gwamnan, Zahara’u Musa ce ta bayyana haka a takardar da ta sama mahannu ga manema labarai.
“A cewar ta shirin na da nufin haɗa kan iyalai, da dawo da martaba, da kuma baiwa ɗaiɗaikun mutane damar dogaro da kansu.
Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa kimamin mutane dubu ɗaya ne za su amfani da wannan shirin na Tallafin biyan Bashi da kayan abinci da kuɗi”.
KU KUMA KARANTA: Matar gwamnan Zamfara ta ɗauki nauyin yi wa mata 100 aikin kansar mama
” Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara ya umarci Hukumar Zakka da tantance waɗanda basusuka ya kaisu gidan gyara hali da ke faɗin Jihar domin biya masu.An kafa wani kwamiti a ƙarƙashin Grand Khadi, tare da Kwanturolan gidajen yari da Malamai, wanda aka dorawa alhakin daidaita basussuka da kuma taimakawa wajen ɗinke matsalar ma’aurata.
Bugu da ƙari, Huriyya Dauda Lawal ta bayar da tallafin kudi da buhunan shinkafa ga wadanda suka ci gajiyar tallafin domin dogaro da kai tare da bukace su da su guji karbar lamuni domin kare mutuncinsu.
“Ina sanar da al’ummar jiharmu cewa mai girma Gwamnan Jihar Zamfara na kokarin ganin an rage wa marasa hali da marasa galihu raɗaɗin da suke ciki a faɗin Jihar.” inji Huriyya.
Jama’a da yawa suka nuna yabo da jin daɗin hakan tare da fatan alheri ga gwamnatin ta jihar Zamfara.