Matakan da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na ƙayyade farashi ba zai kawar da yunwa ba – Masana

0
113

Masana tattalin arziƙi a Najeriya na ganin matakan da gwamnatin ƙasar ke ɗauka da ƙyar za su yi tasiri, idan dai ba an kawo ƙarshen matsalar tsaro da kuma dawo da tallafin man fetur da buɗe iyakoki domin shigowa da abinci cikin ƙasar ba.

‘Yan Najeriya, musanman talakawa na ci gaba da kukan tsada da hauhawar kayan masarufi a kasuwannin ƙasar.

Biyo bayan zanga zangar lumana da wasu mata suka jagoranta a jihar Neja da kuma wasu daban da aka gudanar a jihohin Kano da Osun, ya sa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ɗaukan matakan ba da umarnin fito da tan-tan na abinci da ke runbunan gwamnantin ƙasar, domin karya farashin kayan masarufi da ke neman ya gagari kundila.

To sai dai kuma a cewar wani masanin harkar gona, Farfesa Abubakar Gudigi, na jami’ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a jihar Neja, ya ce da sake a wannan dabara ta gwamnati.

KU KUMA KARANTA:Tsadar abinci: Gwamnati za ta fara raba kayan abinci a faɗin Najeriya – Kwamiti

Gudigi ya ce matakin gwamnati na karya farashi, ba shi zai kawar da yunwa ba, domin yanzu haka akwai waɗanda ke sayen kayan abinci a ƙauyuka, domin sayarwa da tsada, haka kuma dole a karya farashin kayan masarufi da dawo da darajar Naira.

Ko a makon da ya gabata sai da wata kotun tarayya da ke jihar Legas ta umarci gwamnatin Najeriya da ta ɗauki ƙwararan matakai na kawo ƙarshen hauhawar kayan masarufi na kafa hukumar ƙayyade farashin abinci ta kasa.

Wasu ‘yan Najeriya sun cewa akwai buƙatar gwamnati ta ɗauki mataki na dawo da darajar Naira da bunƙasa noma da tattalin arziƙi dama dawo da tallafin man fetur.

A ɓangarensa dai Farfesan harkar Noma Abubakar Gudigi cewa ya yi akwai matakin da gwamnati ya kamata ta ɗauka na hana manyan ‘yan kasuwa shiga ƙauyuka domin saye kayan gona daga manoma.

Yanzu dai a yayin da gwamnati ta ɗauki matakai na rage farashin kayan abinci, abun jira a gani shi ne ko matakan za su taimaka wajen kawo sauƙi ga ‘yan ƙasa.

Leave a Reply