Mataimakin shugaban ‘yan sandan Najeriya ya ziyarci jihar Filato kan matsalar tsaro

Muƙaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, IGP, Kayode Egbetokun, ya kai ziyarar gani da ido a jihar Filato domin duba halin tsaro a jihar.

Mista Egbetokun ya bayyana haka ne a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamna Caleb Mutfwang, ranar Laraba, a gidan gwamnati da ke Jos.

Ziyarar dai na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai kan al’umomin ƙananan hukumomin Mangu da Riyom, da ƙananan hukumomin jihar, da wasu sassan jihar, inda aka ce an yi asarar rayuka sama da 300.

IGP ɗin ya ce rahotannin da ya samu sun nuna cewa hare-haren sun ta’allaƙa ne kan batutuwan siyasa, zamantakewa da tattalin arziƙi, wanda ke buƙatar haɗin kan gwamnati don magance.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe mutane tara tare da ƙona gidaje shida a yankin Filato

“‘Yan sanda na son yin haɗin gwiwa da ku (Gwamna Mutfwang), don shawo kan waɗannan ƙalubale,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa za a shawo kan masu aikata wannan aika-aika tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, inda ya ce; “Na yi imani za mu yi nasara tare.”

Ya amince da ƙoƙarin Muftwang na tallafawa ‘yan sanda wajen gudanar da ayyukansu, yana mai cewa matsalar tsaro wata dama ce ga rundunar ta dawo da martabarta.

Ya ce zai kuma ziyarci wasu sassan jihar a wani rangadin tantancewar da ya yi. Da yake mayar da martani, gwamnan ya godewa IGP bisa ziyarar da ya kai jihar Filato, inda ya ce matakin zai zaburar da mutanensa wajen ƙara himma; sannan kuma zai ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

“Mun yi imanin cewa da zuwanka, da yawa daga cikin jami’an za su tashi zaune, kuma za su iya yin aikinsu gwargwadon ƙarfinsu.

Mutfwang ya ce “Mu a matsayinmu na gwamnati, a shirye muke mu haɗa kai da ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da cewa an kawar da aikata laifuka a Filato.”

Ya ƙara da cewa nasarar da ‘yan sandan suka samu zai zama abin farin ciki ga jama’ar Filato, kuma za a rubuta a cikin kundin tarihi cewa Shugaba Bola Tinubu ya kawo ƙarshen rashin tsaro a jihar.

Ya taya IGP murna bisa naɗin da aka yi masa, ya kuma yaba masa bisa jajircewarsa na magance matsalar rashin tsaro a jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma yi masa fatan samun nasarar gudanar da ayyukansa, sannan ya yi alƙawarin ba shi goyon baya wajen samar da yanayi mai kyau da ‘yan sanda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *