Mataimakin shugaban kwalejin ilimi ta tarayya da ke Potiskum, Dakta Abdulkadir ya rasu
Daga Ibraheem El-Tafseer
Mataimakin shugaban Kwalejin Ilimi Ta Tarayya (Federal College of Education (Technical) da ke Potiskum jihar Yobe, Dakta Abdulkadir Adamu (deputy provost) ya rasu.
Iyalan marigayin sun shaida wa jaridar Neptune Prime cewa, marigayin ya rasu ne a jiya Laraba sakamakon gajeruwar rashin lafiya, a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya ta fannin kiwon lafiya dake Azare, jihar Bauchi (Federal University of Health Sciences Teaching Hospital).
KU KUMA KARANTA:Gini ya rufto akan ɗalibai a GGSTC Potiskum, ɗaliba 1 ta rasu, 5 suna kwance a Asibiti
Ɗaruruwan mutane ne suka halarci sallar jana’izarsa da aka gudanar a fadar mai martaba Sarkin Fika da ke Potiskum. Babban Limamin Masarautar Fika Goni Muhammad Babaji ne ya jagoranci Sallar Jana’izar. Wadanda suka halarci taron sun haɗa da Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali Ibn Muhammad Idriss (Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe).
Abdulkadir ya rasu yana da shekaru 53. Ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya uku. Maryam 14, Muhammad 12 da Khadija mai shekara 6.
Dakta Abdulkadir har zuwa rasuwarsa, ya kasance mataimakin shugaban Kwalejin Ilimi Ta Tarayya (Deputy provost, Administration) kuma daraktan karatun digiri na kwalejin ilimi ta tarayya dake Potiskum jihar Yobe.









