Mataimakin gwamnan Yobe ya buƙaci musulmi da suyi koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammad (SAW)

Daga Sa’adatu Maina, Damaturu

Mataimakin gwamnan jihar Yobe, Alhaji Idi Barde Gubana, a ranar Juma’a ya bi sahun al’ummar Musulmi a babban masallacin na jihar da ke Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yobe, domin gudanar da Sallar Eid-el-fitr (sallah ƙarama).

Babban Limamin Masallacin, Ustas Hudu Mohammad Yusuf ne ya jagoranci Sallar Idi a masallacin da misalin ƙarfe 8:20 na safe.

Da yake gabatar da huɗuba kai tsaye bayan salloli raka’a biyu, Malam Hudu ya yi gargaɗin cewa, Annabi Muhammad (SAW) ya kwaɗaitar da musulmi wajen yin musabaha a tsakanin ‘yan uwa da abokan arziƙi da maƙwabta da kuma ‘yan uwa.

Sannan ya jaddada cewa fa’idar ‘yan uwantaka a Musulunci tana da yawa. Hudu ya buƙaci jama’a da su ci gaba da yin koyi da rayuwar mizani na Annabi Muhammad (SAW) tare da addu’ar zaman lafiya da albarka a faɗin ƙasar nan.

KU KUMA KARANTA: Yadda Uwargida zata sarrafa naman sallah

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai, mataimakin gwamnan jihar Yobe, Idi Gubana ya yabawa al’ummar jihar bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatin Mai Mala Buni mai ci ta hanyar shawarwarin addu’o’i da kuma gudanar da harkokin mulki.

Ya yi ƙira gare su da ka da su yi ƙasa a gwiwa wajen bayar da gudumuwar wanzar da zaman lafiya a jihar.

Ya kuma yi ƙira ga jama’a da su ƙara himma wajen yawaita addu’o’i musamman a wannan lokaci na bukukuwan Sallah da kuma kiyaye muhallin su a koda yaushe.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *