Mata sun yi zanga zanga kan kisan da ɗan sanda yayi wa lauya a Legas

0
437

Gamayyar ƙungiyoyin mata sama da 223 ƙarkashin ƙungiyar Womanifesto sun buƙaci a yi adalci kan kisan da da ɗan sanda mai mukamin ASP, Drambi Vandi ya yi wa wata mace lauya mai ɗauke da juna biyu, mai suna Omobolanle Raheem mai shekaru 41, mamba a ƙungiyar lauyoyin Najeriya a Legas.

ASO Darambi Vandi ya harbe lauyar ne a ranar Kirismeti a lokacin da ta ke hanyarta ta dawowa tare da iyalinta, kisan da ya ɗuki hankalin jama’a da dama a faɗin ƙasar nan.

Yayin da suke bayyana amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba a matsayin “barazana ga rayuwa, ‘yanci, tsaro da kariya daidai a karkashin doka”, matan sun ce akwai tsauraran ƙa’idoji na kasa da ƙasa da ke nuni da yadda ‘yan sanda ya kamata suyi amfani da ƙarfi, ko bindigogi.

“Muna buƙatar a gaggauta gurfanar da Drambi Vandi gaban ƙuliya bisa dokar laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015 da sauran dokokin da suka dace.

“Iyali da abokan mamaciyar, Omobolanle Raheem sun cancanci a yi musu adalci da kuma a biya su ga asarar da suka yi da kuma raunin da suka ji” in ji su.

Babbar daraktan Womanifesto na cibiyar bincike da tattalin arziki na mata, Dokta Abiola Akiyode-Afolabi, ta yi tsokaci ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Adalci ga Omobolanle Raheem da ASP Drambi Vandi ya kashe!’.

KU KUMA KARANTA:Lauya ya yi wa tsohon mijin wacce yake karewa duka a kotu

Baya ga ƙungiyar mata ta WARDC, sauran waɗanda suka rattaba hannun sun haɗa da Women Lobby Group 100, Women Aid Collective, Women’s Rights Advancement and Protection Alternative, Above Whispers Media Foundation, Dr Oby Ezekwesili, Farfesa Adenike Grange, Moji Makanjuola, Saudatu Mahdi, Josephine Effa-Chukwuma, Esther Eghobami , Farfesa Ayodele Atsenuwa, Bisi Fayemi, Farfesa Yinka Omorogbe, Julie Oyegun da Josephine Anienih.

Sauran sun haɗa da Farfesa Funmi Para-Mallam, Ene Obi, Fame Foundation, Ebere Ifendu, Christian Women for Excellence and Empowerment in Nigeria Society, Baobab for Women’s Human Rights and Action Aid, Project Alert on Violence Against Women, Transition Monitoring Group, Nigerian Women Asusun Amincewa da Dorothy Njemanze Foundation.

Womanifesto ta ce ta yi matuƙar kaɗuwa da ƙisan rashin adalci da aka yi wa Raheem, ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar Legas da rundunar ‘yan sandan Najeriya da su gurfanar da ASP Drambi Vandi a gaban kuliya.

Sanarwar ta ce, “Muna kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa, tsantsar gaskiya da kuma sanya ido.

Wannan ire iren kisa ne da yawa da jami’an ‘yan sanda suka yi. Ƙundin tsarin mulkin Najeriya ya ya yi bayani a fili a kan ‘yancin rayuwa na ‘yan ƙasa a matsayin wani muhimmin haƙƙii na ɗan Adam wanda wani ba zai iya ɗaukar rai ba, ba bisa ƙa’ida ba, kuma doka ta kare haƙƙin rayuwa.

“‘Yan sandan Najeriya na yawan amfani da ƙarfi da bindigogi ba bisa ka’ida ba.

“Yin amfani da ƙarfi ba bisa ka’ida ba barazana ce ga rayuwa, ’yanci, tsaro da kuma kariya daidai gwargwado a karƙashin doka.

“Yana da mahimmanci a lura cewa akwai ƙaƙƙarfan ƙa’idodin ƙasa da ƙasa waɗanda ke tafiyar da yadda, da kuma lokacin da ‘yan sanda za su iya amfani da ƙarfi, ko bindigogi; ɗaya daga ciki shi ne ka’idojin Majalisar ɗinkin Duniya kan amfani da ƙarfi da bindigogi da jami’an tsaro ke amfani da su wanda ya ce jami’an ‘yan sanda su yi amfani da muggan makamai ko bindigogi a matsayin mafita ta ƙarshe kuma idan irin wannan ƙarfi ya zama tilas don kare kansu daga hatsarin da ke tafe, rauni da lokacin da babu makawa sai sun yi hakan.

“Kisan Omobolanle abu ne da za a iya kaucewa ko hana faruwar shi.

“Ta yaya za mu tabbatar da wajabcin kashe wata mace mai ciki wadda ta haifi ‘ya’ya biyar da wasu ‘yan uwa a cikin abin hawa?

“Wannan mutuwa ɗaya ce daga cikin yawa da ke faruwa a Najeriya, wajibi ne hukumomin jihohi ciki har da ‘yan sanda su mutunta rai da kuma kare rai ba tare da nuna bambanci ba don haka dole ne rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ɗaukin mutuwar da wasu ire iren ta da dama.

“Dole ne su kawo ƙarshen zalunci da cin zarafi da ‘yan sanda ke yi da gangan waɗanda babban take hakkin ɗan Adam ne” in ji ƙungiyoyin matan.

Sashe na 222 da 223 na dokar laifuka ta jihar Legas (2015) a fili sun bayyana ƙisan kai a matsayin babban laifi da kuma tsara hukuncinsa, sashi na 73 yayi magana akan laifin cin zarafin mulki.

Laifin ASP Drambi Vandi ya tauye ‘yancin rayuwar Omobolanle, ya kuma tauye wa danginta jin daɗin rayuwa.

“A matsayinmu na kungiya, mun ƙuduri aniyar haɗaka da wasu ‘yan Najeriya musamman ƙungiyar lauyoyin Najeriya, domin tabbatar da cewa muna tafiya tare da iyalai da ‘yan Najeriya masu jahar cewa don ganin an yi adalci, muna jajanta wa dangi yayin da muke buƙatar cikakken gyare-gyaren a tsarin ‘yan sanda wanda ke da ɗorewa kuma mai fa’ida ga tsaron jama’a.” In ji su.

Leave a Reply