Masu zanga-zangar ƙarancin naira sun ƙona wasu bankuna biyu a Ogun

0
488

An ƙona bankuna biyu a daidai lokacin da mazauna yankin Shagamu ke nuna rashin amincewarsu da matsalar ƙarancin naira da ake fama da shi a garin na Shagamu na jihar Ogun.

Hotunan bidiyo da aka yaɗa a ranar litinin, sun nuna mazauna da dama suna kallo yayin da aka ƙona bankunan Keystone da Union inda wasu matasa rike da katako ke zanga zangar don nuna adawa.

A ranar Juma’ar makon da ta gabata ne zanga-zangar ta ɓarke a yankin Mowe-Ibafo da ke jihar Ogun, inda jama’a da dama suka tare hanyar Legas zuwa Ibadan, domin nuna adawa da ƙuncin rayuwa da karancin kudin Naira ya janyo.

Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Ogun Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kashe ƙurar zanga-zangar kuma an kame mutum 27 da ake zargi da kintsata ta, ya ce rundunar na gargaɗi ga masu shirya zanga zanga a faɗin jihar.

KU KUMA KARANTA: Yadda ƙarancin naira ya haddasa rikici a Ogun

Harin dai na zuwa ne ‘yan makwanni bayan da ƙungiyar ma’aikatan bankuna, inshora da kuma ma’aikatan kula da harkokin kuɗi (NUBIFIE) ta yi barazanar rufe bankunan kasuwanci a faɗin ƙasar sakamakon ƙaruwar hare-haren da ake kaiwa ma’aikata da kayan aiki da bankuna.

Biyo bayan karancin kuɗin da aka yi wa gyaran fuska na naira, an samu ruɗani a jihohi daban-daban na ƙasar, yayin da ‘yan kasar ke ƙoƙarin musanya tsofaffin takardunsu da sababbi suna cin karo da dogayen layukan kudi a na’urar ATM da tafiyar hawainiya wajen karɓar kuɗaɗen shiga ta yanar gizo.

Hakan ya sa wasu ’yan iskan gari suka mayar da martani cikin fushi tare da kai farmaki a kan ATM na bankunan kasuwanci tare da raunata ma’aikata a cikin lamarin.

Leave a Reply