Masu zanga-zanga sun ɓalle ƙofar Majalisar dokokin ƙasa dake Abuja

Mambobin ƙungiyar ƙwadagon dake zanga-zanga a Abuja da karfin tsiya sun janye babbar kofar majalisar domin shiga harabar Majalisar.

Da farko ‘yan sanda ɗauke da makamai ne suka kulle kofar, bayan wani kazamin rikici da ya ɓarke tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro, wanda daga ƙarshe jama’a suka ci karfinsu.

Ƴan zanga-zangar a lokacin shigar su cikin majalisar

Tun da fari dai KBC Hausa News ta ruwaito cewa mambobin ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC, Trade Union Congress (TUC) da sauran ‘yan Najeriya, sun fito kan titunan Abuja domin nuna adawa da wahalhalun da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ɗauka na cire tallafin man fetur.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *