Daga Ibraheem El-Tafseer
Masu tuƙa Keke NAPEP a Jihar Yobe, sun nuna damuwarsu kan yadda jami’an hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Yobe (YOROTA) suke karɓar kudaɗe daga hannunsu babu gaira babu dalili.
Masu sana’ar tuƙa Keke Napep ɗin, sun koka da cewa a wasu lokutan jami’an na yin kakkausar suka a gare su da cin zarafi da kuma matsa masu da bai kamata ba.
Abubakar Yahaya ɗaya daga cikin masu tuƙa Napep ɗin, ya ce, ‘’Ya kamata gwamna ko kuma shugaban YOROTA ɗin, ya gargaɗi waɗannan jami’an YOROTA ɗin, suna karɓar mana kuɗi, a wasu lokutan kuma su kan yi caje mu, akan laifin da ba mu aikata ba, kusan Naira 40,000 ko Naira 20,000 suna tilasta mana mu biya.
‘’Wasu abokan sana’ar ta mu, da ƙyar suke samun kuɗin ciyar da iyalansu, kuma yawancin Keke Napep ɗin ba namu ba ne. Muna fama da biyan kuɗin ‘balance’ kullum, wasu mako-mako.
KU KUMA KARANTA: Ƙudan zuma sun kusa hana sallar jumu’a a Potiskum
Babagana Tijjani, wani mai tuƙa Keke Napep a Damaturu, ya ce babban abin da ya rataya a wuyan YOROTA shi ne tabbatar da cewa masu ababen hawa sun bi ƙa’idojin zirga-zirgar ababen hawa, amma jami’an ba sa yin abin da aka ɗauke su aiki dominsa, sai suka maida hankali wajen karɓar kuɗaɗe a wajen jama’a.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban YOROTA ɗin, ciki har da ziyarar da ya kai ofishin YOROTA da ke Damaturu don tattaunawa da babban manajan kan wannan zargi, amma abin ya ci tura.