Daga Idris Umar, Zariya
Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Legas ta cafke mutane sama da 50 bayan hargitsin da ya kaure tsakanin wasu matasa da ɓatagari a yankin Ile-Epo da ke jihar Legas.
A sanarwar da kakaknin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ya fitar ranar Alhamis, babban jami’in ɗansanda yankin ya tura jami’ansa zuwa wajen inda kuma tuni aka maido da zaman lafiya.
Sanarwar ta ce an lalata rumfunan da suke zaune.
Kwamihsinan ‘yansanda CP Adegoke Fayoade ya bayar da umarnin a gurfanar da mutanen da aka kama inda kuma ya yi gargaɗi cewa rundunar za ta ɗauki mataki kan duk wanda aka samu da ta da zaune tsaye.
Neptune prime Hausa ta zanta da shugaban ƙungiyar masu kiret na ƙasa kuma sakataren Ƙungiyar masu sayar da abinci na ƙasa Malam Ahmad Alaramma akan yadda lamari ya faru.
Yace matsala ce ta tashi a kasuwar tsakanin wani matashin Bahaushe da wani matashin Bayarabe akan kuɗi ɗan ƙankani.
KU KUMA KARANTA: Za mu raba wa jami’an tsaro tallafin abinci — Gwamnan Kano
Shugaban ya ce akan kuɗi ‘yan ƙalilan ne lamarin ya taso amma sai abin ya koma faɗan ƙabilanci wanda a yanzu an jiwa mutane da dama rauni kuma an ƙona mana Kiret na a ƙalla kuɗi Naira Miliyan ɗari uku da Sittin wanda ba za mu amince da faruwan irin wannan ɓarna ba.
Ƙarshe shugaban ya yi barazanar dakatar da kai Tumatur jihar Legas (Ele epe)
Kuma ya yi ƙira ga gwamnati cewa irin taimakon da ƙungiyar tasu ke bayarwa bai kamata a ce ana yin mata cin zarafi irin haka ba.
Ya tabbatar da cewa a ƙalla ƙungiyar tana da mutane sama da mutum dubbai wanda suke ciyar da iyalansu abinci ƙarƙashin ta wanda haka ya nuna cewa ƙungiyar tana da muhimmanci kuma ta ragewa gwamnati wani aiki.
Kuma ya yi fatan gwamnati za ta sa baki a cikin lamarin.
Bincike na nuna cewa zuwa yanzu hukuma ta shigo cikin lamarin amma ba ta ce komai ba.