Masu gidajen man fetur a Kano sun koka kan rashin ciniki, yayin da masu sayen man suka rage yawan sayayya sakamakon ƙarin farashin man fetur ɗin.
An ƙara farashin man fetur daga Naira 195 zuwa tsakanin Naira 540 zuwa 570 kan kowace lita a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) da ya sa ido a gidajen mai a Kano a ranar Lahadin da ta gabata ya ruwaito cewa, duk da samun man fetur, masu ababen hawa da masu tuƙa babura, amma masu sayan sune kaɗan.
Wasu daga cikin masu gidajen mai fuskokinsu a murtuke cikin ɓacin rai yayin da kasuwancin yake nema ya gagaresu sakamakon rashin ciniki.
Sanusi Adam, dillali ya ce yana samun ƙarancin ciniki idan aka kwatanta da na ɗan lokaci kafin ƙarin farashin.
KU KUMA KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun goyi bayan cire tallafin man fetur
Adam ya bayyana cewa mafi yawan kwastomomi a yanzu suna sayen lita 10 zuwa 20 na man fetur saɓanin lita 30 da lita 50 da suke saya a baya.
Ya ce gidan man nasa ya riƙa kwashe hajarsa cikin kwanaki huɗu kafin ƙarin farashin man.
“Yanzu mako guda ne kuma har yanzu muna da yawan man fetur ba a sayar da shi ba,” in ji shi.
Shi ma wani dillali mai suna Muhammadu Aliyu ya koka kan yadda yawancin kwastomominsa na yau da kullum sun rage yawan sayayya. “Kasuwanci ba ya tafiya kamar da.
Ba mu ƙara samun tallafi kamar yadda muke da shi kafin ƙarin farashin.
“Mutane yanzu sun rage siyayyarsu yayin da wasu suka ɗauki madadin hanyoyin sufuri kamar babura na kasuwanci da kekuna masu uku,” in ji shi.
Sai dai kuma wani mai gidan mai, Idi Garba, ya koka kan halin da kwastomomin suke sayan mai na Naira 3,000 zuwa Naira 5,000 duk da manyan motocinsu.
“Al’amarin ya yi muni. Kamata ya yi gwamnati ta sanar da tallafin domin dillalan man fetur na jin zafi da tashin farashin kayan abinci,” in ji shi.
Sabo Alhassan, wani ɗan kasuwa kuma mai motoci, ya ce tun daga lokacin da aka ƙara farashin man ya kasance yana amfani da babura masu ƙafa uku na kasuwanci domin suna da sauƙin amfani.
Ya ce ba zai iya biyan Naira 27,000 da ake buƙata don cika tankin motarsa ba. Alhassan ya yi ƙira ga gwamnati da ta magance matsalar domin amfanin jama’a tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa abubuwa za su daidaita nan ba da daɗewa ba.