Masu garkuwa da mutane sun kashe wani ɗan kasuwa bayan karɓar kuɗin fansa

1
596

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani ɗan kasuwa a Ugbe, ƙaramar hukumar Akoko ta arewa maso gabashin jihar Ondo, Mista Augustine Okoye, bayan an biya kuɗin fansarsa.

An bayyana cewa an yi garkuwa da Okoye ne tare da matarsa ​​a kan babbar hanyar Isua-Ise a Akoko.

Rahotanni sun ce masu garkuwa da mutanen sun kashe mutumin ne bayan sun karɓi kuɗi a hannun ‘yan uwan sa, sannan suka sako matarsa.

KU KUMA KARANTA:Yadda mata da miji sukayi garkuwa, tare da kashe mai hotel bayan sun karɓi kuɗin fansa miliyan 15

Wata majiya ta ce an kashe shi kafin a biya kuɗin fansa.

Wata majiyar ‘yan sanda a Ikare Akoko, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce an kuɓutar motar waɗanda abin ya shafa daga wurin da lamarin ya faru.

Majiyar ‘yan sandan ta ce jami’an Amotekun da kuma ’yan banga na yankin sun shiga dajin domin gano gawar mutumin, tare da cafke waɗanda ake zargin.

1 COMMENT

Leave a Reply