Masu aikata laifuka suna yin shigar matafiya don ƙwace motoci a Nasarawa

0
338

‘Yan sanda a jihar Nasarawa a ranar Litinin ɗin da ta gabata sun gargaɗi masu ababen hawa da su daina ɗiban baƙi a kan babbar hanya domin a yanzu masu aikata laifuka sun zama matafiya domin ƙwace motoci daga hannun wasu masu ababen hawa da ba a san ko su wanene ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya bayyana haka a garin Lafiya, inda ya ce, ‘yan ta’addan sukan kasance matafiya, kuma suna tsayar da ababen hawa a kan hanyar Lafiya zuwa Abuja da Akwanga-Keffi domin su aikata wannan aika-aika.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta tsare wasu mutane 25 da ake zargi da laifin yin takardar jabu na KAROTA

Rundunar ‘yan sandan ta kuma gargaɗi jama’a da ke tafiye-tafiyen da su tabbatar da zuwa wuraren ajiye motoci da aka ba su izini don hawa ababen hawa domin ka da su faɗa cikin masu aikata laifuka.

Nansel ya ba da tabbacin a cikin sanarwar cewa ‘yan sanda sun ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan barazana.

Ya yi ƙira ga jama’a da suyi amfani da lambobin wayar su: 09115629178, 09067877096, 08112692680, da 08104441179 lokacin da suke cikin damuwa.

Leave a Reply