Marigayi Jimmy Carter na Amurka ya yi tasiri a ƙulla ƙasashe abota a duniya – Masana

0
28
Marigayi Jimmy Carter na Amurka ya yi tasiri a ƙulla ƙasashe abota a duniya - Masana

Marigayi Jimmy Carter na Amurka ya yi tasiri a ƙulla ƙasashe abota a duniya – Masana

A yayin da ake ci gaba da nuna alhini ga mutuwar tsohon shugaban ƙasar Amurka Jimmy Carter, wanda ya rasu yana da shekara 100 a duniya.

Wasu masana siyasa da tsarin mulkin dimokuradiyya sun ce za’a dade ba’a sami zakakurin shugaba irin sa da ya koma rayuwar sa ta da, da ya yi kafin dandana mulki, sakamakon irin tasirin da ya yi a aikin kare kulla alaƙar diflomasiyya, hakkin bil’adama da dabbaka tsarin mulkin dimokuraɗiyya baya ga aikin noma.

Mutuwar tsohon shugaban ƙasar Amurka na 39, Jimmy Carter, mai shekaru 100 a duniya kuma wanda ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, ya sanya dubban mutane a ƙasashen duniya cikin alhini ganin irin tasirin da aka ce marigayin ya yi a fannin kulla alaƙar diflomasiyya, tabbatatar da zaman lafiya, kare haƙƙin bil’adama, noma da dai sauransu.

KU KUMA KARANTA: Amurka za ta ƙara tallafin da take bawa Najeriya

Tuni shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen mika saƙon ta’aziyya da nuna alhini ga rasuwar tsohon shugaban ƙasar Amurka, Jimmy Carter, baya ga gomman masana tarihi, siyasa, dimokuraɗiyya ƙasarsa da suka yi ta jajantawa ƙasar Amurka suna mai cewa an yi rashin zakakurin shugaba.

Najeriya dai na ɗaya daga cikin ƙasashen nahiyar Afirka da marigayi Jimmy Carter ya ziyarta a lokacin da yake shugabanci a ranar 31 ga Maris zuwa 03 ga Afrilun shekarar 1978 a lokacin mulkin tsohon shugaba, Cif Olusegun Obasanjo.

Ko mene ne masana siyasa za su tuna da marigayi Jimmy Carter, Dakta Kichime Goyang Gotau, ya ce a iya sanin sa, ba bu irin shugaba Carter cikin shuwagabanni a kasashen duniya a yanzu.

Masanin tarihi kuma mawallafin jaridar Neptune Prime, Alhaji Hassan Gimba, ya ce zuwan marigayi Jimmy Carter Najeriya a shekarar 1978 na da muhimmanci matuƙa ba ga Najeriya kaɗai ba har da ita kan ta ƙasar Amurka don a lokacin, Amurka na neman karɓuwa a nahiyar Afrika.

A cewar dattijon ƙasa mai shekaru 99 a duniya kuma jigo a siyasar Najeriya tun shekarar 1953, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana cewa ko shakka babu zuwan Jimmy Carter ya ɗaukaka darajar Najeriya a idon ƙasashen duniya.

Masana tarihi da siyasa da dama sun tabbatar da cewa ziyarar marigayi Jimmy Carter ya yi matukar tasiri ga ɗaukaka darajar Najeriya sakamakon cewa shi ne shugaban ƙasar Amurka na farko da ya kawo ziyara Najeriya kuma daga bisani ya ziyarci Laberiya da ƙasar Habasha.

A lokacin da yake kan karagar mulki, marigayi Jimmy ya ziyarci nahiyoyi biyar da suka hada da Afirka, Asiya, Turai, Arewacin Amurka, da Kudancin Amurka.

Cikin ayyukan da marigayi Jimmy Carter ya yi har da na yaki da kwaro ga bangaren noma `11` da bin diddigin ƙuri’u a ƙasashe masu ƙananan ƙarfi lamarin da ya kai shi ga samun kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekara ta 2002, wanda ya biyo bayan cewa shi ne shugaba da ya cimma wata muhimmiyar yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, amma matsalolin tattalin arziki da kuma rikicin garkuwa da mutane na Iran suka yi masa cikas.

Leave a Reply