Manoma a Maiduguri sun roƙi sojoji da su ƙara musu wa’adin aikin gona

0
725

Manoman da ke kan titin Maiduguri- Damboa-Biu da ke wajen birnin Maiduguri a ranar Alhamis sun yi ƙira ga sojoji da su sake duba lokacin da aka basu na damar yin aiki a gonakinsu.

Da dama da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Maiduguri sun ce ƙarfe 11 na safe zuwa ƙarfe 4:00 na yamma, lokacin da aka ba su damar ya kamata a faɗaɗa kuma a ƙara yawan adadin manoma.

“Jami’an tsaro sun ba da katin shiga ga manoma kaɗan, kuma in ba ka da kati, babu manomi da zai iya shiga gonarsa.

KU KUMA KARANTA: Gwamnati ta sasanta tsakanin manoma da makiyayan masarautar Kaltungo a jihar Gombe

“Abin da muke so shi ne a bar manoma da yawa sannan kuma a faɗaɗa lokacin domin manoma su riƙa zuwa gonaki tsakanin ƙarfe 8 na safe da ƙarfe 6 na yamma, ”Abdullahi, wani manomi ya shaida wa NAN.

Abdullahi, ya yabawa jami’an tsaro kan inganta tsaro a yankin. Ya ce hanya mafi dacewa da za a bi domin ganin an inganta harkokin tsaro da kuma sauƙaƙa dawowar al’amura shi ne a sassauta tsauraran matakan tsaro yayin da aka samu sauƙi.

Wani manomi mai suna Malam Modu, ya ce manoman sun damu da yadda makiyaya ke kiwo a gonakinsu da kuma rashin su musamman a lokacin girbi.

“An ce mu bar gonakin da ƙarfe 4 na yamma, sai dai ka yi mamaki yadda a wasu lokuta ake barin wasu makiyaya su yi kiwo a amfanin gonakin mu.

“Lokacin da aka taƙaita ayyukan noma, ya kamata kuma a taƙaita kiwo” Modu ya dage.

Babagoni, Haruna da Lazarus, wasu manoma uku sun bayyana cewa, a wata hanya ta hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, jami’an soji sun bari a fara noma da ƙarfe 7 na safe, kuma ya kamata su riƙa amfani da hanyar Maiduguri zuwa Biu.

Sun buƙaci da a riƙa yin taro akai-akai tsakanin jami’an tsaro da manoma domin cimma matsaya guda.

“Jami’an tsaro wani lokaci suna ba manoma taƙaitaccen sanarwa don kammala girbin su kuma a cikin haka sai da yawa suka girbe amfanin gona da ba su kai ga yi ba,” in ji Haruna.

Wani jami’in tsaro da ya zanta da NAN bisa sharaɗin sakaya sunansa ya ce dukkanin matakan da aka ɗauka na kare muradun manoma ne.

“Wasu watannin baya babu wanda ya isa ya kuskura ya yi noma a wannan yanki; amma tare da ingantaccen yanayin tsaro, ana barin da yawa damar shiga gonakinsu, amma tare da wasu ƙuntatawa.

“Ya kamata manoma su yi haƙuri. Da lokaci komai zai yi kyau a gare mu duka,” kamar yadda ya shaida wa NAN.

Leave a Reply