Manhajar ‘Threads’ da yadda ake amfani da ita

Daga Ibraheem El-Tafseer

‘Threads’ sabuwar manhaja ce (application) dangogin su Facebook, Instagram da Whatsapp. Manhajar Threads ta yi kama da Twitter sosai. Sai dai akwai abubuwa da suke da bambamci da Twitter. A Twitter adadin haruffa 280 ne za ka iya rubuta su, amma a Threads an ba ka damar rubuta haruffa 500. A Twitter bidiyo mai tsawon daƙiƙa 20 ne za ka iya ɗora wa, amma a Threads za ka iya ɗora bidiyo mai tsawon minti biyar. A Twitter za ka iya yin tattaunawa da juna (chatting), amma a Threads a babu wannan damar.

Yadda ake yin rijista shi ne, za ka je ‘play store’ ko ‘app store’ ka sauƙe shi. Sai ka yi rijista. Amma dole sai kana da account da Instagram, sannan za ka samu damar yin rijista da Threads ɗin.

KU KUMA KARANTA: Yadda za ka kare shafinka na Facebook da Twitter daga masu ƙwace

Mutum miliyan goma ne suka yi rijista don amfani da sabuwar manhajar Thread a cikin sa’a bakwai da ƙaddamar da ita, in ji shugaban kamfanin Meta, Mark Zuckerberg.

Ya bayyana dandalin da cewa kishiya ce “da za ta yi zaman mutunci” da Twitter, wadda hamshaƙin mai arziƙin nan Elon Musk ya saya a watan Oktoba.

Ƙwararru sun ce dandalin Threads zai iya jan hankalin masu amfani da Twitter waɗanda ba sa farin ciki da sauye-sauyen da aka kawo wa manhajar a baya-bayan nan.

Threads na bai wa mai amfani da ita, damar wallafa haruffa sama da 500, kuma tana da siffofi irin na Tuwita.

Tun farko, Mista Zuckerberg ya ce gudanar da dandalin “mai sauƙin kai ga masu amfani… zai kasance muhimmin lamari wajen samun nasarar manhajar”.

Sai dai Mista Elon Musk ya mayar da martanin cewa: “Tabbas ya fi sauƙi, wasu baƙin ido su far maka a Tuwita, da mutum ya ɓuge da ƙaryar samun farin ciki daga Instagram na ɓoye.”

Katafaren kamfanin Meta wanda ya mallaki shafin Facebook da Instagram ne, ya ƙaddamar da manhajar sada zumunta da muhawarar, mai suna Threads, da galibi ake kallo a matsayin kishiya ga Twitter.

Ba ma ga ƙwararrun da ke kallon ƙaddamar da sabuwar manhajar ta Threads a matsayin kishiya ga Twitter mallakar Elon Musk ba, Mark Zuckerberg da kansa ya furta cewa Threads wanda ya ƙunshi abubuwa kusan irin na Twitter zai iya yi wa Tuwita fintinkau.

Duk da yake, zuwa yanzu ba a ƙaddamar da sabuwar manhajar sada zumunta da muhawarar a yankin Tarayyar Turai ba, amma Mista Zuckerberg ya ce a cikin sa’a huɗu da ƙaddamar da shi har ya samu masu amfani da shi sama da miliyan biyar.

Ya ƙara da cewa zai ɗauki lokaci kafin sabon dandalin ya buwaya, amma dai mai yiwuwa ne Threads ya samu yawan mutane sama da miliyan dubu ɗaya.

A cewar Zuckerberg, Twitter ya samu wannan damar, sai dai bai yi amfani da ita ba. Amma ya ce su suna fatan za su yi.

Sai dai abokan gogayya sun yi suka a kan yawan bayanan masu amfani da ita da manhajar za ta riƙa tattarawa.

A ciki akwai batun lafiya da na kuɗi da kuma bayanan mai shiga shafin , in ji rumbun Apple Store.

A yanzu dai ana iya sauƙe wannan manhaja ta sabon shafin na sada zumunta da muhawara na Threads, a sama da ƙasashe 100, ciki har da Birtaniya, amma ban da ƙasashen Tarayyar Turai.

Kamfanin Meta da ya mallaki wannan sabuwar manhaja ya ce, a yanzu zubin farko ce, wanda hakan ke nufin akwai ƙarin wasu abubuwa da ya shirya sanya wa manhajar domin ƙara jan hankalin jama’a

Kasancewar shafin na da alaƙa da Instagram wanda ke da tarin mabiya, wannan zai sa ya samu sauƙin ɗaukar hankalin tarin miliyoyin mabiya da ke kan Instagram, waɗanda tuni wasu ma har sun daɗe da sauƙe shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *