Malamin addini ya buƙaci a saka shugabannin addini cikin harkokin mulki

0
650

Wani malamin addinin musuluncin mazaunin Kano, Sheikh Mahajjadina Sani Kano ya bayar da shawarar sanya malaman addini cikin harkokin mulki a kowane mataki na gwamnati a Najeriya.

Ya kuma buƙaci sabbin shugabannin majalisar dokokin ƙasar da su samar da yanayin yadda malaman addini za su bayar da gudumawa mai ma’ana ga harkokin mulki a ƙasar nan.

Sani Kano ya ce malaman addini za su iya zama masu tsaka-tsaki wajen fuskantar munanan ɗabi’u a tsakanin matasan Najeriya.

Ya yi wannan ƙiran ne a zantawarsa da jaridar LEADERSHIP a Abuja.

KU KUMA KARANTA: Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa, ya doke Yari

Ya ce ƙiran nasa ya zama wajibi saboda yadda ake amfani da malaman addini, inda ya ce ana buƙatar su daƙile rashin ɗa’a a cikin al’umma.

Malamin ya ce munanan ɗabi’u irin su satar waya da lalata da a ƙarshe su kan sa matasa su zama masu sauƙin kai wa ga zama manya a laifuka kamar ta’addanci, ‘yan fashi da tayar da ƙayar baya shugabannin addini za su iya magance su.

Sani Kano, don haka ya buƙaci jihohin da ta’addanci suka addabi ƙasar da su sanya malaman addini wajen tunkarar matsalar.

“An gwada wannan kuma an gano yana da tasiri a ƙasashe da dama na duniya, don haka ya kamata Najeriya ma ta bi wannan hanya domin ayyukan ‘yan ta’adda su zama tarihi a ƙasarmu,” inji shi.

Leave a Reply