Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi

Daga Ibraheem El-Tafseer

Masu zanga-zangar sun fito ne daga manyan addinan ƙasar biyu – Musulunci da Kiristanci.

Shugabannin addinai a Malawi sun jagoranci zanga-zangar nuna adawa da auren jinsi a ranar Alhamis, tare da ɗaruruwan mutane a Blantyre, babban birnin Malawi, domin nuna rashin amincewarsu da abin da suka ƙira yunƙurin halatta auren jinsi a ƙasar.

Masu zanga-zangar sun fito ne daga manyan addinan ƙasar biyu – Kiristanci da Musulunci.

Babban limamin coci, Thomas Luke Msusa ne ya jagoranci zanga-zangar a Blantyre. Ya ce auren jinsi zunubi ne, kuma halatta irin wannan auren zai kai ga musibar gushewar bil’adama.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta kama mata 15 da suka halarci bikin ‘yan luwaɗi a Kano


Ya ce “idan muka canza yadda muke rayuwa a matsayin iyali, hakan na nufin za mu ƙare baki ɗaya.” “Idan muka ci gaba da aurar da namiji da namiji, tabbas za mu kasance babu zuri’a, babu ‘ya’ya, ba rayuwa a duniya, ba rayuwa a Malawi.”

Luwaɗi laifi ne a Malawi kuma hukuncinsa shi ne aƙalla ɗaurin shekaru 14 a gidan yari.

Duk da haka, ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana damuwarsu game da wariyar da ‘yan maɗigo, luwaɗi, auren jinsi da sauran ‘yan kungiyar (LGBTQ) ke fuskanta a cikin ƙasar.

Michael Kaiyatsa, babban daraktan cibiyar kare haƙƙin bil’adama, ya ce malaman addini na da ‘yancin gudanar da zanga-zanga kan duk wani abu da suke ganin laifi ne, amma kuma ya kamata su yi la’akari da haƙƙoƙin sauran ƙungiyoyi.


Comments

2 responses to “Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Malaman addini a Malawi sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da auren jinsi […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *