Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin Tinubu ta dakatar da yarjejeniyar Samoa

0
68
Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin Tinubu ta dakatar da yarjejeniyar Samoa

Majalisar wakilai ta buƙaci gwamnatin Tinubu ta dakatar da yarjejeniyar Samoa

Majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta dakatar da yarjejeniyar Samoa da ta tayar da ƙura a ƙasar.

A zaman da ta yi yau Talata, majalisar ta ce ya kamata a dakatar da yarjejeniyar har sai gwamnati ta fito ta bayyana ɓangarorin yarjejeniyar da suka haifar da cecekuce.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Aliyu Madaki wanda ya tabbatar wa da BBC da matakin ya ce majalisar ta kuma nemi ministocin da suka jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar su gurfana gabanta tare da takardun yarjejeniyar domin buƙatar fayyace komi musamman “ɓangaren da ke bayani kan daidaiton jinsi.”

Yarjejeniyar Samoa da gwamnatin Najeriya ta sanya wa hannu da Tarayyar Turai ta tayar da ƙura a Najeriya inda wasu ƴan ƙasar da dama suka nuna fushinsu musamman zargin cewa yarjejeniyar na ƙunshe da wani ɓangare da ke nuna goyon baya da kuma kare muradun masu maɗigo da luwaɗi.

KU KUMA KARANTA: Tinubu na shirin zuba tiriliyan 2 don bunƙasa tattalin arziki

Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta musanta, inda ministan kasafin kudi da tsare-tsare da kuma ministan watsa labarai suka ce Najeriya ba za ta taɓa amincewa da wata yarjejeniyar da ta saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar da kuma al’adu da addinin ƙasar.

Leave a Reply