Majalisar tattalin arziƙin Najeriya ta goyi bayan kafa ‘yansandan jihohi

0
28
Majalisar tattalin arziƙin Najeriya ta goyi bayan kafa 'yansandan jihohi

Majalisar tattalin arziƙin Najeriya ta goyi bayan kafa ‘yansandan jihohi

Majalisar tattalin arziƙi ta Nijeriya wadda ta ƙunshi dukkan gwamnonin ƙasar ta amince da ƙudurin kafa ’yansandan jihohi a kowace jiha domin tunkarar matsalolin tsaro da ya dabaibaye ƙasar.

Majalsar ta ɗauki wannan matakin ne a wani zama da ta yi jiya Alhamis a fadar Shugaban kasa ta Aso Rock karkashin jagorancin mataimakin Shugaban kasa Kashim Shetimma. Kudurin da aka sake gabatarwa a taron majalisar tattalin arzikin kasa (NEC, ya sami goyon bayan akasarin gwamnonin jihohin

A hirar shi da Muryar Amurka bayan taron, gwamnan jihar Kaduna Uba Sani wanda ya yi magana da yawun gwamnonin ya bayyana cewa, sun yanke wannan hukuncin ne ganin yadda matsalar tsaro ta ta’azzara, da kuma karancin jami’an tsaron da ake fuskahnta, da ake bukata idan ana so a iya shawo kan wannan matsalar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa, “dukan jihohi 36 sun gabatar da rahotonsu da aka bukata su rubuto kan maganar kirkiro Rundunar ‘yan sanda na jiha,..kusan dukan gwamnonin jihohin 36 sun yarda cewa, yin ‘yan sanda na jiohohi shi zai kawo karshen wannan matsala da ake fama da ita.”

KU KUMA KARANTA:‘Yan sanda sun kama wani da ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta

Gwamnan ya kara da cewa,” akwai a kalla mutane miliyan 230 a kasar, kuma idan aka duba sojojin da ke kasar duka basu wuce dubu 250 ba. ‘Yan sandan kasar kuma ba su wuce dubu 370 ba, idan aka hada su za a ga akwai matsaloli.”

Bisa ga cewarshi, “akwai wurare a kasar da za a yi tafiya ta kilomita, 30, 50, 100 ba ka ga jami’in tsaro ko kwaya daya ba.”

Ya bayyana cewa, “dan sandan jiha, zai ba ‘yan sandan dama su rike makamai, irin su AK47, wanda doka ba ta ba da dama ga ‘yan sa kai su rike makamai manya manya da bindigogi ba.”

Gwamna Uba Sani ya ce, harkar ‘yan sanda na jiha yana da abubuwa da dama da suka hada da cewa, “galibinsu su ‘yan jihar ne. sun san yanayin wurinsu.”

Bisa ga cewarshi, za a tsaida shawara a kan batun a watan Janairu shekara ta 2025.

Idan aka tsaida shawarar aiwatar da tsarin, kirkiro da rundunar ‘yan sandan jihohin za su ba jihohi damar kafa hukumomin tilasta bin doka don magance barazanar tsaro da su ke fuskanta a matsayin jiha yadda ya kamata.

Leave a Reply