Majalisar tattalin arziƙi za ta yi aiki da ƙungiyar ƙwadago kan cire tallafin man fetur

0
199

Daga Ibraheem El-Tafseer

Majalisar Tattalin Arziƙin, wadda mataimakin shugaban ƙasa ke jagoranta, ta ƙunshi gwamnonin jihohin ƙasar 36.
Majalisar kula da Tattalin Arziƙin Najeriya ta ce ta ɗauki wani mataki na tunkarar matsalar cire tallafin man fetur a ƙasar, inda ta kafa wani kwamitin wucin gadi.

Babban manufar kafa kwamitin ita ce fara tattaunawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na jihohi daban-daban don samun mafita.

A yayin taron majalisar karo na 135 a Abuja ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne aka yanke shawarar kafa kwamitin.

Kwamitin ya ƙunshi shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, AbdulRahman AbdulRazaq da Gwamnan jihar Anambara, Chukwuma Soludo da Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Hope Uzodinma na jihar Imo da Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Bala Mohammed na jihar Bauchi, da gwamnan jihar Abiya, Alex Otti.

KU KUMA KARANTA: Za mu bai wa Google goyon baya don samar da ayyukan yi miliyan ɗaya ga ‘yan Najeriya – Tinubu

Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa aikin kwamitin shi ne haɗa kai da shugabannin ƙungiyar ƙwadago a faɗin Najeriya domin samar da mafita mai amfani ga ƙasar bayan cire tallafin man fetur.

Bugu da ƙari, majalisar ta NEC ta samu bayanai kan yadda ake ci gaba da raba muhimman kayayyaki a faɗin ƙasar baki ɗaya kamar shinkafa da hatsi da takin zamani ga jihohi.

An kuma amince da matakin ba da tallafin kuɗi naira biliyan biyar daga gwamnatin tarayya, tare da jinjina wa babban bankin Najeriya (CBN) da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) bisa gudunmawar suke takawa game da waɗannan tsare-tsare.

Hukumar ta kuma amince da ƙoƙarin da gwamnatocin jihohi ke yi a nasu aikin, tare da ƙara musu ƙwarin gwiwar faɗaɗa rabon kayan agaji domin rage wahalhalun da ‘yan ƙasa ke ciki musamman talakawa masu ƙaramin ƙarfi.

Majalisar ta kuma miƙa ta’aziyya ga rundunar sojojin Najeriya da iyalansu kan kisan da aka yi wa wasu dakarunta a jihar Neja tare da yin shiru na minti ɗaya don karrama mamatan.

Leave a Reply