Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin 2025 kan naira tiriliyan 54

0
23
Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin 2025 kan naira tiriliyan 54

Majalisar dokokin tarayyar Najeriya ta amince da kasafin kuɗin 2025 kan naira tiriliyan 54

Kasafin ya ƙunshi ƙarin kuɗin shiga da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana samu a wasiku biyu da ya aika wa Majalisar, iinda ya daga Kasafin daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.99 bayan gabatar da kasafin kudin kasa tun cikin watan Disamba. Wasu na ganin haka ya saba yadda ake gabatar da kasafin kudin kasar kamar yadda za ku ji a wannan rahoto.

Tun ranar 18 ga watan Disamba da Shugaba Bola Tinubu ya mika kasafin Naira triliyan 49.7 Majalisar ke ta aiki tare da Ma’aikatu da hukumomin gwamnati wajen daidaita kasafin da kuma yadda za a kashe kudi.

Abin da ya dauki hankali shi ne a ranar 5 ga watan Fabrairun nan sai Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya daga kasafin kudin daga Naira Tiriliyan 49.7 zuwa Tiriliyan 54. 2, inda ya bayyana karin kudaden shiga da wasu manyan hukumomin gwamnati ke samu, inda ya mika gyarar kasafin ta wasu wasiku guda biyu daban daban da ya aika wa Majalisar Dattawa da ta Wakilai wadanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta na Majalisar Dattawa shi kuma Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya karanta na Majalisar Wakilai.

A cewar ShugabaTinubu, karin kudin da aka samu ya kai Tiriliyan 1.4 daga Hukumar Tara Haraji ta Kasa wato FIRS, da Tiriliyan 1.2 daga Hukumar Kwastam ta Najeriya da kuma Tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka samu.Shi ne ya kawo jimlar kasafin zuwa Naira Tiriliyan 54.99.

KU KUMA KARANTA:Ƙungiyar USAID ce ta ɗauki nauyin ƙungiyar Boko Haram – Ɗan Majalisar Dokokin Amurka

Dan Majalisar Wakilai daga mazabar Gumi da Bukuyum ta Jihar Sokoto, Suleiman Abubakar Gumi, ya yi bayani cewa wannan kasafi shi ne kasafin da zai farfado da tattalin arzikin kasa har al’umma su mora domin shi ne kasafi mafi girma da aka taba yi a kasar. Suleiman ya ce kasafin ya kunshi komi da komi da zai taba rayuwar ul’umma, kama daga harkar tsaro, da noma da ilimi da kiwon lafiya da kuma yadda za a tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu. Suleiman ya ce a hankali al’umma za su ga yadda rayuwar su za ta sauya.

A nashi nazarin, Dan Majalisa Wakilai Daga Jihar Bauchi, Auwalu Abdu Gwalabe, ya koka ne cewa ana ta yin kasafin kudin ne amma talakawa ba sa ganin sa a kasa, domin a yanzu kasafi iri hudu ake aiwatarwa a lokaci daya. Auwalu ya ce duk da cewa wannan shi ne kasafi mafi girma a tarihin Najeriya, talaka ba ya ganin sauyi.

Ko me ya sa Shugaba Tinubu ya kara yawan kasafin cikin gaggawa a daidai lokacin da ‘yan Majalisa ke aiki akai, a maimakon ya kawo shi a matsayin kwaryakwaryar kasafi daga baya? Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, ya yi bayani cewa kudin da aka samo din na al’umma ne, shi yasa Tinubu ya ce a hada shi da kasafin kudin bana domin a kashe wajen farfado da rayuwar ‘yan kasa. Mohammed ya ce wannan shi ne irin banbancin da Shugaba Tinubu ya ke so ya nuna wajen farfado da tattalin arzikin kasar cikin lokaci domin a samu sauyi mai ma’ana a kasa.

A farkon wannan shekara ne aka fara aiwatar da kasafin kudin shekara 2024 kuma ana sa ran kammala shi a watan Yuni na shekarar 2025 kafin a kai ga aiwatar da sabon Kasafin na bana.

Leave a Reply