Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar kafa hukumar tsaro ta jiha

0
44
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar kafa hukumar tsaro ta jiha

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da ƙudirin dokar kafa hukumar tsaro ta jiha

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da kudirin kafa hukumar tsaro mallakin jiha.

Matakin ya biyo bayan zazzafar muhawara akan wasu muhimman batutuwa a cikin ƙudirin, ciki har da wani batu na haramta shigar da ƴan siyasa cikin shugabancin hukumar.

KU KUMA KARANTA:Za mu yi bincike kan kisan da aka yi wa mutane a Rimin Zakara – Gwamnatin Kano

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husaini Dala, ya bayyana cewa majalisar ta yi zuzzurfan nazari kan kudirin dokar don tabbatar da cewa ya amfani ko wanne ɓangare a jihar.

“Dokar za ta bai wa jami’an tsaron ikon rike makami, kama mutane, hana aikata laifi, da kama masu laifi a fadin jihar Kano,” in ji Dala.

Ya kuma ba da tabbacin cewa bisa ga tanade-tanaden doka, za a ba da ragamar hukumar a hannun wadanda ba yan siyasa ba.

Leave a Reply