Majalisar dokokin jihar Kaduna za ta fara binciken El-Rufai

0
164

Daga Idris Umar, Zariya

Majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata ta kafa kwamitin mutane 13 da zai binciki yadda aka gudanar da hada-hadar kuɗi, lamuni, bayar da tallafi da gudanar da ayyuka a ƙarƙashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-rufai.

Hon. Yusuf Mugu ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙaura ne ya gabatar da ƙudirin domin a binciki bayanan bashin da tsohon gwamnan ya karɓo.

KU KUMA KARANTA: El-Rufai ya bar wa jihar Kaduna ɗimbim bashi – Gwamnan Uba Sani

Kakakin majalisar, Hon. Yusuf Ɗahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman majalisar, ya buƙaci kwamitin da ya gayyaci duk masu ruwa da tsaki domin yi musu tambayoyi da kuma bincike kan lamarin.

Leave a Reply