Majalisar Dattawa ta amince shugaban ƙasa ya aro Naira Tiriliyon 1.77

0
10
Majalisar Dattawa ta amince shugaban ƙasa ya aro Naira Tiriliyon 1.77

Majalisar Dattawa ta amince shugaban ƙasa ya aro Naira Tiriliyon 1.77

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince Shugaban kasar, Bola Tinubu ya ranto naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da dokar kasafin kuɗin bana daga ketare.

Za a yi amfani da rancen wajen cike gibin Naira tiriliyan 9.7 dake cikin kasafin kuɗin na bana.

A ranar Talata Shugaba Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin ƙasar, da wasiƙar neman sahalewa ya ranto bashin Naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da dokar kasafin kudin bana.

Haka kuma, Shugaba Tinubun ya aike da matsakaicin kasafin da za’a kashe tsakanin 2025 da 2027 ga majalisar tare da ƙudirin neman yin garambawul ga shirin tallafawa al’ummar ƙasar, da nufin mayar da kuɗin bayanan ‘yan ƙasa ya zama abinda gwamnatin tarayya za ta rika amfani da shi wajen aiwatar da shirye-shiryenta na ba da tallafi.

KU KUMA KARANTA: Majalisa ta amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki

Hakan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan babban bankin Najeriya ya bayyana cewar gwamnatin kasar ta kashe dala bilyan 3.58 wajen biyan basussukan da ake binta a ketare a watanni 9 na farkon shekarar 2024 da muke ciki.

Leave a Reply