Majalisa ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Ningi
Majalisar Dattawan Najeriya ta yafe wa Sanata Abdul Ahmed Ningi tare da janye dakatarwar da ta yi masa tun daga ranar 12 ga watan Maris.
Majalisar ta ɗauki matakin ne bayan Sanata Abba Moro ya gabatar da ƙudirin neman afuwarta a madadinsa kuma “ya ɗauki alhakin dukkan” abin da ya faru a zaman da suka yi yau Talata.
Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya siffanta Ningi a matsayin “mai hazaƙa” kuma ya ce sun ɗauki matakin ne “ba tare da nuna ɓangaranci ba”.
KU KUMA KARANTA: Majalisa ta dakatar da sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku
Dakatarwar da aka yi wa sanatan mai wakiltar Mazaɓar Bauchi ta Tsakiya ta tsawon wata ta jawo cecekuce a majalisar da ma faɗin ƙasar a watan Maris.
Ƙudirin da majalisar ta zartar a lokacin ya zargi Abdul Ningi da “zubar da ƙimar majalisa” bayan ya zargi shugabanninta da sake yin wani kasafin kuɗi na 2024 bayan wanda ‘yan majalisar suka amince da shi a bainar jama’a.