Mai tsaron lafiyar ministan ƙwadago a Uganda, ya harbe ministan

A ranar Talatar da ta gabata ne wani mai tsaron lafiyarsa na soji ya harbe ƙaramin ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi da masana’antu a ƙasar Uganda Charles Engola.

An bayyana cewa Mista Engola yana shiga motarsa ​​ne domin tafiya aiki sai mai gadin ya harbe shi. Rundunar ‘yan sandan Uganda a yayin da take musayar bayanan farko game da kisan ministan, ta ce an kashe marigayin ne da misalin ƙarfe 8:00 na safe a unguwar Kyanja da ke birnin Kampala.

Kakakin ‘yan sandan Uganda, Fred Enanga, ya ce, “Ɗaya daga cikin masu gadin ministan ne ya yi harbin, wanda kuma ya yi harbi da dama a kusa da wajen.

“Da ya yi harbin ya gudu daga wurin zuwa cibiyar kasuwanci da ke Kyanja Ring Road inda ya shiga wani salon ya harbe kansa.”

KU KUMA KARANTA: An harbe babban malamin Shi’a na Majalisar Ƙwararrun Iran

Mista Enanga ya ce an fara binciken ne a matakin farko. Ya ƙara da cewa “Mun aike da ƙwararru a fagen aikata laifuka waɗanda za su yi amfani da na’urorin zamani don tantance ainihin musabbabin kisan.”

Rahotanni sun bayyana cewa, shaidun gani da ido sun ce sojan na sojojin Ugandan ya koka kan rashin biyansa albashi da kuma cin zarafinsa kafin ya harbe kansa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *