Mai sana’ar POS a Kano ya mayar da naira miliyan 10 da aka tura masa bisa kuskure

0
115

Wani mai sana’ar POS a Unguwar Kurnar Asabe da ke Jihar Kano ya mayar da kusan naira miliyan 10 da wani kwastomansa ya yi kuskuren tura masa a maimakon dubu 10.

Lamarin dai ya faru ne yayin da abokin kasuwancinsa ya yi yunƙurin tura wa mai POS ɗin naira dubu 10, kamar yadda rundanar ’yan sanda Kanon ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne tun a watan Disamba na shekarar 2023, lokacin da mai sana’ar POS mai suna Mohammed Sani Abdulrahman ya fahimci cewa wani kwastomansa wanda ya karɓi naira dubu 10 daga wurinsa ya tura masa naira miliyan 10 bisa kuskure.

Daga nan ne sai mai POS ɗin mai shekaru 37 ya garzaya hedikwatar ’yan sandan Kanon ya sanar da su abin da ya faru.

KU KUMA KARANTA:A yi gaggawar gudanar da bincike kan zargin da Sanata Ningi ya yi – Atiku

Sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce sun kwashe kimanin wata uku suna bincike kafin su gano mutumin wanda ɗan kasuwa ne a Kasuwar Dawanau da ke Kano.

Rundunar ’yan sandan ta ce tuni mai POS ɗin ya mayar wa kwastoman kuɗinsa naira miliyan tara da dubu dari tara da casa’in.

Sai dai jin daɗin haka ya sa ɗan kasuwar ya ba mai POS ɗin kyautar naira 500,000.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Muhammad Usaini Gumel ya yabawa Sani mai POS bisa gaskiya da amana da ya nuna a harkar kasuwancinsa.

Leave a Reply