Mai rainon jariri ta saci jariri ɗan wata biyu lokacin yaye ɗalibai a makaranta a Kwara

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne aka sace wani jariri ɗan watanni biyu mai suna Usman Idris daga hannun mahaifiyarsa a yayin bikin yaye ɗalibai a garin Ilorin na jihar Kwara.

Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa wata mata da aka baiwa amanar kula da jaririn ta ɓace ne da misalin ƙarfe 3:00 na rana a yayin bikin yaye ɗaliban da aka gudanar a harabar makarantar da ke unguwar Sawmill a Ilorin.

Mahaifiyar yaron mai suna Sekinah, ta tabbatar wa LEADERSHIP da ke Ilorin faruwar lamarin a ranar Lahadi.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun kama wani mutum da ya sace jaririya ‘yar wata tara a Imo

Ta bayyana wanda ake zargin a matsayin wata mace doguwa kuma fara, sanye da rigar ankara purple da baƙin gyale.

“Ta zo wurina kimanin makonni biyu da suka wuce tana son koyon yadda ake haɗa kayan ciye-ciye.

Na karɓe ta amma ban san ko ɗaya daga cikin danginta ko inda ta tsaya ba kuma ba ni da ma lambarta.

“Mun je bikin yaye yaron tare kuma ta ce za ta taimake ni in ɗauki jaririn a lokacin da na raka babban ɗana da ke kammala karatunsa a wajen bikin karɓar takardar shaidarsa.

“Wannan shi ne na ƙarshe da muka gani game da ita.

Mun kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na ‘A’ da ke Surulere, Ilọrin amma har yanzu ba mu ji ta bakinsu ba,” inji ta.

A halin da ake ciki, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ba a samu damar jin ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.


Comments

2 responses to “Mai rainon jariri ta saci jariri ɗan wata biyu lokacin yaye ɗalibai a makaranta a Kwara”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Mai rainon jariri ta saci jariri ɗan wata biyu lokacin yaye ɗalibai a makaranta a Kwara […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Mai rainon jariri ta saci jariri ɗan wata biyu lokacin yaye ɗalibai a makaranta a Kwara […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *