Mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki

0
108
Mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki

Mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aiki

Ajuri, ya bayyana hakan ne a wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.

“A ranar Juma’a, na miƙa takarda ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, inda na ke shaida masa cewa na tafi hutu na sai-baba-ta-gani domin mayar da hankali kan batun rashin lafiya wanda hakan abun damuwa ne ga ahali na.

KU KUMA KARANTA:Shugaban hukumar tattara bayanan sirri na ƙasa ya yi murabus

”A yayin da na ke godiya kan wannan nauyi da aka dora min wanda yanzu ya kai matakin yanke shawarar dakatawa da aikina a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai kuma mai magana da yawunsa; jakada na musaaman ga shugaban kasa a fannin sauyin yanayi kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan shirin Evergreen.

“Na dau wannan matakin ne bayan tuntubar iyalina a yayin da rashin lafiya ya tsananta a gida na.

Zan dawo bakin aiki da zarar waraka ta samu kuma lokaci ya bada dama,” in ji Ngelale.

Leave a Reply