Mahukuntan DR Congo sun yiwa fursunoni 1,200 afuwa da zummar rage cunkoso
Mahukunta a Jamhoriyar Dimokradiyar Congo, sun cimma matsayar yin afuwa ga fursunoni 1,200 da ke tsare a babban gidan yarin Makala na ƙasar da zummar rage cinkoson fursunoni, lamarin da aka ce na zuwa ne bayan kafa wani kwamitin da ya yi bincike, da niyyar kawo sauyi gami da inganta gidajen Kurkukun ƙasar .
A ranar lahadin nan ne dai Ministan Shari’ar Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, Costant Mutamba, ya sanar da aniyar gwamnatin ƙasar na rage yawan wadanda ke tsare a gidan yarin Makala da ke babban birnin ƙasar, Kishasha, saboda rage cunkoson da ake samu a gidan yarin.
Sai dai kuma a cewar Ministan za’a yi hakan ne, rukuni rukuni, inda za’a fara da mutane 400 a duk mako, kuma haka lamarin zai ci gaba har zuwa lokacin da za a kammala.
Tuni ministan ya amince da a saki rukunnin farko, wanda ya ƙunshi fursunoni 421, bayan a tabbatar da cancantarsu na samun yanci, kuma sun zauna a kurkun aƙalla fiye da rabin wa’adin zaman su.
KU KUMA KARANTA: Fursunoni sun tsere daga gidan yarin Nijar da ke tsare da masu ta da ƙayar baya
Kafin cimma wannan matsayar, sai da aka kafa kwamitin da zai yi bincike kan fursunonin a game da ɗabi’unsu dan gano cancantarsu na samun ‘yanci, amma banda waɗanda aka tsare bisa lafin sace dukiyar al’umma, a cewar ministan.
Shi dai Kurkukun Makala, an ginashi ne dan Fursunoni 1,500 a shekarar 1957 amma yanzu ake tsare da fursunoni 15,000, kamar yadda wasu bayanai suka nuna.