Mahadi Shehu ya chaccaki tsohon shugaban Najeriya, Buhari

Fitaccen mai kwarmata bayanai game da zargin cin hanci da rashawa a Najeriya, Mahadi Shehu ya yiwa tsohon shugaban Najeriya Muhammad Buhari zagin tsamar nama a shafinsa na X (Twitter) kamar yadda WikkiTimes Hausa ta gani.

Mahadi Shehu ya yi wannan zagin ne a matsayin martani ga furucin tsohon shugaban Najeriya da ke ya ke cewa yana murna da ƙarin kuɗin man fetur da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi.

Abin da Mahadi Shehu ya wallafa a shafinsa na X

Tsohon banza, azzalumi, mara tausayi, butulu. Yadda ka saka bayin Allah a cikin ƙunci, sai ka ga ƙunci a rayuwarka. Lokacin mutuwarka kuma sai Allah ya maida maka mugun ƙudirinka. Allah ya isar mana a kanka”. In ji Mahadi Shehu

Duk cewa Mahadi Shehu bai ambaci sunan tsohon shugaban Najeriyar ba, amma ya sanya hotonsa tare da yin zagin tsamari mama ga Muhammadu Buhari ɗin.

A jiya ne dai shafin DCL Hausa ya wallafa wani faifan bidiyo mai tsayin daƙiƙa talatin da aka jiyo tsohon shugaba Muhammadu Buhari yana cewa “Alhamdulillah na dawo gida kuma na yi murna da Tinubu ya ƙara kuɗin fetur“.

Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2021 ne gwamnatin Jihar Katsina ta gurfanar da Mahadi a kotu bisa zarginsa da ɓata mata suna da tunzura mutane bayan ya zargi gwamnatin da almubazzaranci da kuɗin da aka tanada don samar da tsaro.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *