Mafi akasarin bindigogin da ke hannun ‘yan ta’adda na gwamnati ne – Ribadu

0
42
Mafi akasarin bindigogin da ke hannun ‘yan ta’adda na gwamnati ne - Ribadu

Mafi akasarin bindigogin da ke hannun ‘yan ta’adda na gwamnati ne – Ribadu

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha’anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya zargi wasu ‘yansanda da sojoji da sayarwa da ‘yan ta’adda makamai ko ba su haya, irin makaman kuma da ake amfani da su wajen hallaka jami’an
tsaron.

Mallam Nuhu Ribadu wanda ke jawabi yayin gangamin lalata bindigogi kimanin 2,400 da hukumar hana yaduwar makamai ta Najeriya ta yi a wajen birnin Abuja, ya ce duk jami’in tsaron da zai sayar wa da ‘yan ta’adda makami to tabbas wannan ya wuce kidnapa ko dan Boko Haram

Dama dai an dade ana zargin wasu baragurbin jami’an tsaro na sai dawa ‘yan ta’adda makamai, zargin da hukumance mashawarcin shugaban kasa kan tsaron ya tabbatasr da shi, yana mai cewa:

”Eh, yana faruwa, tabbas yana faruwa, bindigogi masu yawan gaske da ke hanun ‘yan ta’adda ainihinsu na gwamnati ne, haka siddan a dauka a sayar da ko ba da su haya, wannan wane irin masifa ce? dole a dakatar da hakan, dole mu yaki ire-iren wadannan shaidanun jami’ai.”

KU KUMA KARANTA:Ba mu tura jami’an tsaro masarautar Kano ba – Nuhu Ribadu

Mallam Nuhu Ribadu ya ce akwai kuma wasu mutane can wata nahiya suna kekkera makamai suna kawo mana wannan nahiyya don mu karkashe junanmu.

Ya kuma buga misali da abin da ke faruwa a yankin Sahel wanda ya ce na fama da matsalar da ba wani yanki a duniya da ke fama kamarsa, inda mutane ke cikin yunwa, amma sai ake kawo masu makamai suna hallaka junansu, maimakon a kawo masu ci gaban kimiyya don inganta rayuwarsu.

Tunda farko sai da shugaban hukumar hana yaduwar kananan makamai ta Najeriya DIG Babatunde Kokuma ya yi bayanin cewa an samo makaman ne daga hanun ‘yan ta’adda ta hanyar soji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro, da ma wanda ‘yan ta’addan da suka yi saranda suka mikawa hukuma, sannan nan gaba kadan za a lalata makaman da hukumar kwastam ta cafke

A cewar masanin tsaro Kwamishinan ‘yansanda Rabiu Ladodo kamata ya yi a yi wa jami’an tsaro adalci domin ba duk bindigar da ke hanun dan ta’adda ne ta jami’an tsaro ba.

Leave a Reply