Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnatin Yobe ta kafa kwamitin mutane 10

0
23
Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnatin Yobe ta kafa kwamitin mutane 10

Mafi Ƙarancin Albashi: Gwamnatin Yobe ta kafa kwamitin mutane 10

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni CON, ya amince da kundin tsarin mulki na kwamitin mutane 10, kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da shi kwanan nan.

Kwamitin mutane goman wanda sakataren gwamnatin jihar zai jagoranta yana haɗa da shugaban ma’aikatan gwamnati a matsayin shugaba, yayin da sauran za su kasance mambobi.

Mambobin kwamitin sun haɗa da kwamishinan kuɗi, Alh. Mohammed Abatcha Geidam, kasafin kuɗi da tsare-tsare na tattalin arziki Alh. Garba Gagiyo, ƙaramar Hukuma da Masarautu, Alhaji Ibrahim Adamu Jajere FCNA, da Akanta-Janar na Jiha.

Sauran sun haɗa da shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Comrade Mukhtar Musa Tarabutu da TUC Bulama Musa yayin da sakataren dindindin kan ƙaddamarwa, Shuaibu Ibrahim Amshi da na ofishin ma’aikatan gwamnati na shugaban ma’aikata Alh Dakta Bukar Kilo mni, za su kasance sakatare da haɗin gwiwa.

KU KUMA KARANTA: Ƙarin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na dubu 70 — NLC

Kwamitin mutum goman zai kasance a cikin wasu sharuɗɗan dabaru kan nasarar aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa a cikin jihar.

Kwamitin zai kuma tantance al’amuran kuɗi na aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi a Jiha da ƙananan Hukumomi ba ya ga bayar da shawarwarin da gwamnati za ta duba.

Leave a Reply