Ma’aikatar Ilimi ta jihar Yobe ta ba da lasisi ga makarantu masu zaman kansu

0
136
Ma'aikatar Ilimi ta jihar Yobe ta ba da lasisi ga makarantu masu zaman kansu

Ma’aikatar Ilimi ta jihar Yobe ta ba da lasisi ga makarantu masu zaman kansu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Ƙungiyar makarantu masu zaman kansu ta ƙasa (NAPPS) reshen Potiskum jihar Yobe, ta shirya taron ƙarawa juna sani na wuni ɗaya a garin Potiskum jihar Yobe.

Maƙasudin manufar shirya taron shi ne raba lasisi ga makarantu masu zaman kansu da ke ƙarƙashin NAPPS, wanda ma’aikatar ilimi ta jihar Yobe ta ba su.

Shugaban NAPPS reshen Potiskum Malam Muhammad Sambo Adam ya bayyana cewa, “idan za a iya tunawa a shekarar 2024 ma’aikatar ilimi ta jihar Yobe a ƙarƙashin kwamishinan ma’aikatar ilimin sakandire ta jihar Yobe, ta soke tare da cire lasisin duk wasu makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar”.

Ya ƙara da cewa, “Bayan ganawa da dama da ma’aikatar ilimi a birnin Damaturu, kwamishinan ya amince tare da raba fom ga dukkan makarantu masu zaman kansu, wanda ya zama dole makarantun su bi matakan cike fom ɗin sannan a mayar wa ma’aikatar.

KU KUMA KARANTA: Sabbin masana’antun sarrafa Riɗi a Yobe, za su ƙara samar da tan dubu 6

A ƙarshen jawabinsa, shugaban NAPPS, ya shawarci makarantun da ba su mayar da fom ɗinsu ba, da su gaggauta miƙa shi, domin samun lasisin nasu daga ma’aikatar.

Akwai makarantu masu zaman kansu sama da 150 a ƙaramar hukumar Potiskum. Hakan ya sa Potiskum ta fi kowacce ƙaramar hukuma yawan makarantu masu zaman kansu a jihar, amma makarantu 29 ne kawai suka karɓi lasisi.

An gudanar da taron ne a yau 19 ga watan Fabrairu, a makarantar Mori Memorial, bayan NTA Potiskum. Daraktocin makarantu da dama sun halarci taron.

Leave a Reply