MƊD ta saki dala miliyan 5 a cikin shirye-shiryen ambaliyar ruwa, amsa gaggawa a Najeriya
Mai tsara taimako na gaggawa na ƙungiyar MƊD, Tom Fletcher, ya ba da dala miliyan biyar daga Central Emergency Fund (CERF) don ɗaukan mataki na ɗan lokaci ga ambaliyar da ke ƙasar Najeriya.
Mai tsara ayyukan agaji na MƊD a Najeriya, Mohamed Malick Fall, ya yi wannan sanarwar a ranar 12 ga fabrairu, 2025, a Abuja.
Mista Fall ya ce “yin tsammani da kuma yin aiki kafin matsaloli kamar rigyawa suna ceton rai. Yana kuma taimaka wajen kare abincin mutane wanda kuma yana rage rashin lafiyarsu”.
“A cikin yanayin duniya wanda ake kare da rage kudade don ayyukan jin kai, wannan matakin yana da matukar muhimmanci domin baya rage mafi munanan tasirin gaggawa kawai, yana kara taimakawa wajen rage tsadar kudin amsa ga jin kai.”
KU KUMA KARANTA: MƊD ta ƙaddamar da bugu biyu na ;Muryoyin Sahel;
Rabon dala miliyan 5 na CERF yana tallafawa ƙoƙarin da gwamnati ke jagorantawa ta hanyar ƙungiyar aikin tsinkaya na gaba. Ƙungiyar aikin tana haɗa muhimman hukumomi ciki har da Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMET), Hukumar Hidimar Ruwa ta Najeriya, da Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa karkashin kulawar Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. Wannan yana cikin haɗin gwiwa da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya na Kula da Ayyukan Jin Kai (OCHA).
A Duniya gaba ɗaya, OCHA wanda ke sarrafa CERF da Kudade na Ƙasashe (CBPFs) kamar Asusun Jin Kai na Najeriya (NHF), yana jagorantar aikin tsinkaya na gaba yana taimakawa miliyoyin mutane ta hanyar magance haɗari irin su ambaliyar ruwa, fari, guguwar iska da kuma cutar amai da gudawa.
A watan Oktoba na shekarar 2024, CERF ta saki dala miliyan 5 don ƙara yawan amsa ambaliyar ruwa da magance bukatun gaggawa a jihohin Borno da Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya, da Jihar Sakkwato a arewa maso yamma.
Kuɗaɗen CERF sun taimaka tare da rabon dala miliyan 6 daga NHF (wanda ya haɗa da dala miliyan 2 don aikin tsinkaya wanda aka fitar tare da manyan ambaliyar ruwa da suka tilasta kusan mutane 400,000 a Jihar Borno).
Daidai da hasashen Yanayi na 2025 na NiMET, ana sa rai cewa damina zai fara a jihohin arewa kamar Bauchi, Borno, Jigawa, Kano, Katsina, Sakkwato, Yobe da Zamfara, daga farkon Yuni zuwa Yuli 2025.
Wannan lokacin ya dace da lokacin yunwa (lokacin tsakanin girbi) inda rashin abinci da ƙarancin abinci suke ƙaruwa tare da ambaliyar ruwa da yaduwar cututtuka irin su amai da gudawa. Shirye-shiryen da suka dace a kan waɗannan haɗurran na iya yiwuwa suna da matukar muhimmanci.
Shirin Bukatun Jin Kai da Amsar Gaggawa na Najeriya na shekarar 2025 (HNRP), ya fitar da wata hanya mai ma’ana ta tsinkaya ta hanyar sadaukar da kashi 5 cikin 100 (dala miliyan 45) daga jimlar bukatu (dala miliyan 910) don aikin tsinkaya. Wannan rabon kudade na CERF ya wakilta kawai kashi 11 cikin 100 na bukatun don aikin tsinkaya. Ana buƙatar ƙarin kuɗi cikin gaggawa don ƙara yawan aikin.