Likitan bogi da ya ɗinke mahaifa da mafitsarar wata mace ya shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta cafke wani mutum mai suna Olelekan Rabiu mai shekaru 31 da haihuwa, wanda ake zargi da nuna kansa a matsayin likita kuma babban likitan asibitin Iremide Private, da ke Orita Ojo a ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Oyediran Oyeyemi, ya gurfanar da wanda ake zargin tare da wasu mutane uku a gaban manema labarai a ranar Juma’a a garin Akure.

Oyeyemi ya bayyana cewa, a ranar 20 ga watan Disamba ne wata tawagar jami’an ‘yan sanda ta musamman, suka kama wanda ake zargin, a lokacin da aka samu rahoton rashin ɗa’a a kansa.

Kwamishinan ‘yan sandan ya ce wanda ake zargin ya yi wa wata mata mai juna biyu aikin tiyatar (an sakaya sunanta) wadda daga baya aka garzaya da ita asibiti saboda yawan zubar da jini daga al’aurarta.

“An gano cewa likitan da ya bayyana kansa, ya ɗinke mahaifa da kuma wajen fitsari.

“A binciken da ake yi, an gano cewa wanda ake zargin ba likita ba ne, amma ya halarci makarantar fasahar lafiya ta Ijebu-Ode, inda ya yi karatu a matsayin ma’aikacin lafiyar jama’a. “Kuma ya kasance yana yaudarar mutane da cewa shi likita,” in ji shi.

Yayin da yake zantawa da manema labarai, Olalekan Rabiu ya amince cewa shi ma’aikaci ne a fannin kiwon lafiyar al’umma, inda ya ce ya shafe shekaru bakwai yana wannan sana’a.

Ya ce, yayi aikin cikin nasara a lokacin da ya yi wa matar da ake magana a kai, bayan kwana 27 ta dawo ta yi korafin zubar jinin.

Ya ce a baya ya yi aiki guda ɗaya cikin nasara, ya ce ya fara aikin tiyata ne a lokacin da ɗan uwansa ya saya masa gidan sama a shekara 2015.

“A gaskiya, ni ba likita ba ne amma na yi karatu a matsayin ma’aikacin lafiyar jama’a a makarantar lafiya ta Ijebu Ode da ke jihar Ogun.

“Duk da cewa, ina da ƙoƙari a layin kuma babu mai taimako, da zan koma makaranta amma yanzu ina shirin komawa makaranta,” in ji shi.

A cewarsa, an kawo matar asibitisa, wanda yayansa ya sai masa a shekarar 2015, ya ce, bayan da ya duba matar, ya gano cewa ba za a iya haihuwa da kanta ba.

“Bayan na duba lafiyarta, na bayyana wa ‘yan uwanta halin da take ciki, domin na duba sakamakon nata na duban dan tayi na gano tana cikin mako na 43 da ciki.

KU KUMA KARANTA:Hukumar ‘yansanda sun ceto mutane 77 daga coci a Jihar Ondo

Ita ma jaririyar ta riga ta jigata, aka ba ni izinin yi mata tiyata don ceto matar da jaririyar.

“Don haka, lokacin da ta dawo bayan kwana 10,dan na duba lafiyarta, sai na gano cewa ba ta shan magani, kuma ba ta da tsafta.

“Bayan an shafe kwanaki 27 da yi mata tiyata, sai ta sake dawowa tana korafin zubar jini, domin ceto rayuwarta, don haka nan take, na mika ta zuwa cibiyar kula da masu fama da cutar da ke garin Ondo.

Ya ƙara da cewa, “Ina son mutane su taimake ni, ina da mata mai ɗauke da juna biyu na wata tara a gida yanzu, na yi alƙawarin ba zan ƙara ba,” inji likitan bogin.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *