Likita ya naushi marar lafiya a yayin aikin tiyata

Duk inda marar lafiya yake a duniya tarairayarsa ake yi ballantana a asibiti ko uwa-uba ɗakin tiyata inda ake ƙoƙarin ceto ransa.

Sai dai ba haka ta kasance ba ga wani likita, wanda aka zarga da nannaushin wata marar lafiya a lokacin da yake tsaka da yi mata tiyata a ido.

Wannan lamari ya faru ne a ƙasar Chana ga wata tsohuwa mai shekara 82 lokacin da likitan ke yi mata aikin ido.

Likitan wanda ba a bayyana sunansa ba ya dunƙule hannu ne ya naushe ta har sau uku cikin fushi.

Rahotanni sun ce tsohuwar ta riƙa motsa idonta ne da kanta saboda rashin tasirin allurar kashe laka a jiki domin yin tiyata, wanda hakan ya sa ta rika yin motsi likitan na tsaka da yi mata tiyata.

An ce likitan ya rika yi mata gargaɗi kafin a karshe ya naushe ta a fuska har su uku.

KU KUMA KARANTA: An yankewa mahaifiya hukuncin ɗaurin rai da rai, bisa laifin kashe ‘yarta

An ce tsohuwar ba ta fahimci abin da likitan ke faɗa ba, kasancewar ba ta jin harshen Mandarin wanda yake mata tsawa da shi, kuma hakan ya kai ga naushin ta, inda kyamarar CCTV ta ɗauki lamarin kuma wata likita ta yaɗa wa duniya a dandalin sada zumunta, haka ya fusata dubban mutane a ciki da wajen ƙasar.

Ɓullar wannan bidiyo ya sa Hukumar Asibitin mai suna Aier Chaina amsa cewa lallai lamarin ya faru a ɗaya daga cikin asibitocinsu a garin Guigang da ke Kudu maso yammacin ƙasar, kimanin mil 300 yamma da Tsibirin Hong Kong.

Sanarwar da asibitin ya fitar ta ce tuni ta dakatar shugaban asibitin da kuma likitan da ake zargi da naushin, wanda aka ce ya ji mata rauni a fuska.

Kuma a cewar ɗanta hakan ya sa yanzu ba ta gani da ido ɗaya, sai dai ba a sani ba ko sakamakon naushin ne ko kuma haka ta je asibitin.

“Bayan hakuri, sun ba mu Yuan 500 (kimanin naira 775,00) na ban baki dangane da abin ya faru,” in ji dan wadda aka nausa.

Dokta Ai Fen wacce ta fitar da bidiyon, fitacciyar likita ce kuma ɗaya daga cikin likitocin da suka kwarmata ɓullar cutar Kwarona a garin Wuhan, ta yi hakan ne bayan ta ci karo da bidiyon da asibitin da ma’aikatansa suka ja bakinsu suka yi shiru a kai, tun faruwar lamarin a watan Disamban shekarar 2019.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *