Lauya ya yi wa tsohon mijin wacce yake karewa duka a kotu

4
361

Wani lamarin mai ban mamaki da ya abku a kotun sashin iyali ta Milimani na ƙasar Kenya ya ɗauki hankalin jama’a bayan da wani lauya ya daddage ya yi wa tsohon mijin matar da yake karewa dukan tsiya a kotu.

Lamarin da ya faru a ranar Laraba, 16 ga Nuwamba, yayin da lauyan ya ci zarafin ɗan kasuwan wanda matar sa ta yi ƙararsa kan kula da yaransu.

Robert Asembo wanda ke wakiltar matar wacce kuma ma’aikaciyar gwamnati ce, ya yi wa tsohon mijin nata duka da mari a wajen zauren kotun Alƙali Robert Mbogo.

Tsohuwar matar na neman tsohon mijinta ya bata kuɗi sama da Ksh dubu 600 domin kula da yara.

Faɗan dai ya ɓarke ne a lokacin da suke jira a wajen kotun, jim kaɗan bayan lauyan ya zargi ɗan kasuwar da gayyatar wasu ‘yan jarida don su yaɗa barin domim cutar da matar da yake karewa.

4 COMMENTS

Leave a Reply