Kwanan nan za mu kawo ƙarshen Bello Turji da tawagarsa – Janar Chris Musa

0
92
Kwanan nan za mu kawo ƙarshen Bello Turji da tawagarsa – Janar Chris Musa

Kwanan nan za mu kawo ƙarshen Bello Turji da tawagarsa – Janar Chris Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya bayyana cewar lokaci ya kusa ƙurewa jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda kasancewar dakarun sojin ƙasar sun himmatu wajen kawo ƙarshen rashin tsaro a Zamfara da ma yankin arewa maso yamma baki ɗaya.

Babban hafsan tsaron ya bayyana hakan ne a jihar Zamfara, da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya, a wata keɓaɓɓiyar hira da Muryar Amurka.

KU KUMA KARANTA:Rashin tsaro: Gwamnan Yobe ya gana da babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya

Ya kuma tabbatar da hallaka ƙasurgumin dan ta’addar nan Halilu Sububu da ya addabi jihar Zamfara a matsayin wata nasara da dakarun suka samu.

Kasurgumin dan ta’addar ya gamu da ajalinsa ne a Kwaren Kirya, wani kauye a karamar hukumar Maru.

Leave a Reply