Kwanaki 100: Jagorancin Asma’u A Matsayin Shugabar NUJ Kaduna Ta Yi Tasiri

0
337

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KAMAR ba a taba yin irinsa ba, Kungiyar yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kaduna ta samu gagarumin ci gaba, musamman a fannin samar da yanayi mai kyau ga mambobinta wanda a halin yanzu ke taimaka wa kwararru da kwazon da ake bukata daga kwararrun ‘yan Jaridu, kuma babu shakka yanayin kwanciyar hankali ya haifar da wani matakin mutunta kungiyar.

Asma’u Yawo Halilu, ta kasance a cikin tarihi, kasancewarta mace ta farko da ta fara shugabantar kungiyar NUJ Kaduna, kuma ta biyu a fadin kasar nan. A matsayin mace mai tarihi; Asma’u tana yunƙurin rubuta sunanta da zinare a matsayin mai hazaka, tare da irin nasarorin da aka samu a bayyane a cikin kwanaki 100 na aikinta, wanda ko shakka babu Asma’u ta kasance zakaran gwajin dafi.

Ƙarfinta, ƙwazo a ofis, ikhlasi na zuciya da manufa, balaga wajen tafiyar da al’amura, da kasancewarta mai kwazo musamman wajen tunkarar batutuwan da suka shafi jin daɗin membobinta sun riga sun tabbatar da furcin nan da ya ce: ‘Abin da namiji zai iya yi, mace za ta iya yin fiye da hakan, idan aka yi la’akari da yanayin hangen nesanta.

Kamar yadda ta ce a lokacin yakin neman zabenta, burinta shi ne tabbatar da cewa dukkan ‘ya’yan kungiyar NUJ ta Kaduna sun samu tasirin shugabancinsu da kuma tabbatar da kwarewa, kuma sun yi alkawarin samar da yanayi mai kyau ga mambobin kuma zasu cika su a hankali domin a bayyane suke.

Acewarta, ” Jin dadin mambobinsu ne hanyar budin su a matsayinmu na shugabanni, hakazalika ba da fifiko ga jin dadin Jama’a ba shakka zai mayar da Kungiyar zuwa lokutan daukaka da girmamawa a tsakanin mambobinta,” in ji Asma’u.

To sai dai kuma duk wanda ke da masaniyar Kungiyar NUJ ta Kaduna kafin zuwa Asmau Yawo Halilu a cikin kwanaki 100 da suka gabata, na iya shaida cewa yanayin shugabancin ta na kan turbar da ta dace domin kuwa a yau duk wanda ya zo Sakatariyar ta NUJ, tambayar farko a bakinsa ita ce wane ne ke Shugabantar cibiyar Kungiyar NUJ ta Kaduna?

A cikin mafi kankanin lokaci, an dawo da kwarin gwiwar membobin wanda hakan ya biyo bayan bayyana gaskiya da rashin rikon sakainar kashi na shugabancinta, wanda acewarta “Gaskiya da rikon amana ne abin lura a shugabancinmu, hadin kan ‘ya’yan Kungiyarmu ma shi ne abin da na sa a gaba, addu’armu ita ce Allah Madaukakin Sarki Ya kiyaye mu Ya kuma yi mana jagora Ya ba mu damar cika alkawuran yakin neman zabe da muka daukarwa al’ummarmu,” in ji Asma’u.

Hankalin Asmau da sanin ya kamata da kasancewarta mai kirki mai ruhin afuwa da kokarin hada kan al’ummarta su ne kyawawan dabi’un da suka ja hankalin ‘yan Kungiyar zuwa gare ta, kuma babu shakka Asma’u ta kasance mai canza wasa, shugaba mai kishin kasa da hangen nesa wanda a halin da ake ciki na shugabancinta, ta samar da ofishi ga kungiyar masu aiko da rahotanni a Sakatariyar kungiyar NUJ Kaduna.

“Dalilin da ya sani wannan tunanin shi ne don inganta haɗin kai a tsakanin mambobinmu. Kuma bayan haka, ba abin jin dadi ba cewa kungiyar na kokawa don biyan kuɗin ofishin haya. Hakazalika a yanzu muna kuma aiki a kan Kungiyar Mata Yan Jaridu wato (NAWOJ), ta yadda ‘yan Jarida mata za su iya samun ofishin nasu a cikin ita Sakatariyar ta NUJ, domin hakki ne a kanmu a matsayinmu na shugabanni mu tabbatar da cewa mambobinmu suna aiki yadda ya kamata,” inji ta.

Ta ci gaba da cewa, harkokin wasanni na Kungiyar da suka yi fama rashin kulawa da aka yi watsi da su na tsawon shekaru za a dawo da su, yayin da aka fara aiki kan yadda ake samun Gidan Wasanni, domin burin Asma’u shi ne a samu gidan Wasanni mai cike da kayan aiki na zamani kuma tuni wannan yunkurin ya fara kankama.

“Wadannan halaye ne da muka gani a Asma’u, kuma muna farin cikin ganin alkawuran da ta yi na yakin neman zabe ana aiwatar da su daya bayan daya, muna da imanin cewa za ta iya yin abin da ya dace da goyon bayan mambobin wanda ayyukanta sun ba mu mamaki. A cikin wannan dan karamin lokaci, ta taka rawar gani sosai,” in ji tsohon shugaban cibiyar Kungiyar Yan Jaridu na Kamfanin NNN, Nicholas Dekera.

Har ila yau, a karon farko a tarihin kungiyar NUJ ta Kaduna, karkashin Jagorancin Asma’u ta gabatar da Thrift and Co-operative Society ga mambobi Kungiyar NUJ. Haka kuma bayyanar sabbin shuwagabannin an sake dawo da kwas na Cibiyar Nazarin Jarida ta Duniya (IIJ) wacce aka dakatar da ita na tsawon shekaru.

A cikin wannan lokacin, Ƙungiyar ta kuma haɗa gwiwa da Kamfanin lemon kwalba ta 7up domin sake yin fentin Sakatariyar wanda cika sharuddan ya sanya sabon salo ga Sakatariyar.

Har ila yau, a kwanakin baya ne dai salon Shugabancin Asma’u ya baiwa kungiyar damar samun wata mota kirar Ford galaxy, wanda Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Malam Uba Sani ya bayar. Hakazalika an gudanar da horon jagoranci ga wasu mambobin kungiyar zartaswa na Jiha (SEC) da gidauniyar ci gaban kafofin watsa labarai ta Afrika (AMDF) ta yi, wanda wannan wani mataki ne na jagorancin Asma’u.

Shugaban kungiyar FRCN, Umar Adamu Sarkin Fada, ya bayyana cewa, ” horon kan Jagoranci ya samu nasara wajen tsara tunanin shugabannin Kungiyar nasu kan yadda za su jagoranci al’ummar su.

Kafin fitowarta, babu wani bandaki guda ɗaya mai aiki, (toilet) a cikin sakatariyar membobin Kungiyar. Sai dai a yau labari ya sauya inda sabbin shugabannin da Asma’u ta ke jagoranta suka inganta bandakin da aka yi watsi da su domin amfanin al’ummar.

A bisa irin nasarorin da aka gani kuma aka rubuta ya zuwa yanzu, ai ko makaho ma na iya ji, wato a takaice yanzu ba labari bane cewa kasancewar Asma’u Yawo Halilu a matsayin shugaba, Daniel Duniya mataimakin shugaba, Gambo Santos a matsayin sakatare, Salisu Ibrahim a matsayin Auditor, Gabriel Idibia a matsayin Ex-officio 1 da Matata Abdullahi a matsayin Ex-officio. 2, tuni suna jagorantar Kungiyar izuwa ga nasara.

A cikin wannan ‘Tafiya ta Canji’, kyakkyawar manufa Asma’u ya riga ya sanya Kungiyar a kan wani matsayi na kishin samun nasara.

Leave a Reply