Kwamitin Tsaro na MƊD zai kaɗa ƙuri’a kan tsagaita wuta a Sudan gabanin watan Ramadan

0
172

Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya zai kaɗa ƙuri’a a ranar Juma’a kan yin kira da a tsagaita wuta a Sudan, a daidai lokacin da za a fara azumin watan Ramadan a mako mai zuwa, yayin da lamura ke ci gaba da taɓarɓarewa a ƙasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, daftarin ƙudurin da aka shirya zai yi kira ga dukkan ɓangarorin da su ɗauki matakin dakatar da rikicin ba tare da ɓata lokaci ba kafin watan Ramadan, lokacin da ya kamata ya zama na ibdar azumi da addu’a da tunani ga Musulman duniya.

Har ila yau, ta yi ƙira ga ɓangarorin da ke faɗa da juna da su ba da damar kai agajin jinƙai ba tare da wata tangarda ba ta kan iyakoki da kuma filin daga.

A zaman da kwamitin sulhun ya yi a ranar Alhamis, Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira ga dukkan bangarorin Sudan da su mutunta darajar watan Ramadan ta hanyar dakatar da yaƙi a cikin watan mai alfarma.

KU KUMA KARANTA: Ana yi wa yara fyaɗe sakamakon yaƙin da ke faruwa a Sudan – MƊD

Ya ƙara da cewa, “Dole ne tsagaita wuta ta haɗa da daina ɓrin wuta a duk faɗin ƙasar, tare da samar da tabbatacciyar hanya wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa ga al’ummar Sudan.”

Guterres ya yi gargaɗi game da bala’in jinƙai da ake ciki da kuma ƙaruwar barazanar yunwa.

Daga baya Biritaniya ta sanar da cewa za ta nemi wani ƙuduri da zai sake ɗaukaka ƙorafin nasa.

An fara gwabza yaƙin ne tun ranar 15 ga Afrilun 2023.

An dai yi artabu da sojojin Janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun sa-kai na gaggawa na Janar Mohamed Hamdan Daglo, wanda shi ne na biyu a fagen soja

Hakan ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma wasu miliyan takwas da suka rasa matsugunansu, fiye da yadda wani rikici ya jawo a duniya.

Yayin da akasarin mambobin Kwamitin Tsaro a ranar Alhamis suka goyi bayan kiran tsagaita wuta na watan Ramadan, wasu tawagogin sun yi gum da bakinsu, musamman na China da Rasha.

Ita ma Kungiyar Tarayyar Afirka AU a wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a ta kuma yi kira ga ɓangarorin Sudan da ke rikici da juna da su tsagaita wuta a fadin kasar baki daya a cikin watan Ramadan.

Shugaban AU, Moussa Faki Mahamat, ya ce tsagaita wuta na iya taimakawa wajen aikewa da kayan agaji ga fararen hula da ke cikin mawuyacin hali.

Leave a Reply