Kwamandan mayaƙan Boko Haram da wasu mutum 5 sun miƙa wuya ga sojoji a Borno

0
103

Kwamandan mayaƙan Boko Haram da wasu mutum 5 sun miƙa wuya ga sojoji a Borno

Masu tada ƙayar bayan sun yi watsi da ayyukan ta’addanci tare da miƙa wuya ga sojojin ne a jiya Alhamis 23 ga watan Mayun da muke ciki.

Mayaƙan Boko Haram 6 ciki har da kwamandan ‘yan ta’adda sun miƙa wuya ga dakarun Rundunar MNJTF, ta haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Da yake bayyana hakan a cikin wata sanarwa, babban jami’in yaɗa labaran rundunar ta MNJTF, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, ya bayyana sunan kwamandan ‘yan ta’addar da Adamu Muhammad.

Ya kuma zayyano sunayen sauran ‘yan ta’addar da Isah Ali mai shekaru 18 da Hassan Modu ɗan shekara 18 da Nasir Idris mai shekaru 23 dogarin kwamanda Jubilaram, Usman Rash da Abba Aji mai shekaru 21 da kuma Abubakar Isah ɗan shekara 20.

A cewar sanarwar, “‘yan ta’addar sun tsere daga maɓoyar tsagin ISWAP dake Jubilaram, dake shiyar kudancin tafkin Chadi.

KU KUMA KARANTA:Shugaban sojojin Isra’ila ya amince da shirin kai hari a Rafah

Adamu mai shekaru 22, ya taka rawa a hare-hare da dama da aka kai kuma ya karaɗe garuruwan Kangarwa da Alagarno da Doro Naira da Dogon Chikwu dake ƙaramar ƙungiyar hukumar Kukawa ta jihar Borno”.

A cewar kakakin Rundunar ta MNJTF, fiye da ‘yan ta’adda 100 ne suka tuba tun bayan da aka ƙaddamar da aikin wanzar da zaman lafiya na tsaftace yankin tafkin Chadi mai laƙabin “Operation Lake Sanity” a turance wanda manufarsa ita ce kakkaɓe masu tada ƙayar baya daga yankin.

Yace tun daga ranar 23 ga watan afrilun da ya gabata, masu tada ƙayar baya 119 ne suka miƙa wuya tare da yin ƙira ga takwarorinsu su rungumi tafarkin zaman lafiya tare da ajiye makamai.

Leave a Reply