Kungiyar AFAN Reshen Jihar Jigawa Ta Sami Takardar Yabo Ta “Media Action”

0
351

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

SABODA namijin kokarin da kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa keyi na hada kan manoman Jihar da kuma tabbatar da cewa ana zaman lafiya tsakanin su da sauran bangarori, kafar sadarwa ta “Media Action-Nigeria” ta damka takardar yabo ga kungiyar tare da yaba irin shugabancin da ake yiwa kungiyar.

A cikin takardar yabon “Media Action-Nigeria” ta bayyana cewa kungiyar manoma ta Jihar Jigawa ta kasance daya daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu da take aiwatar  da abubuwa wadanda suke  bunkasa zaman lafiya da kaunar juna musamman a wannan lokaci da ake ciki na bukatar dogaro dakai.

Haka kuma kafar sadarwar ta sanar wa kungiyar cewa an gudanar da bincike na lokaci mai tsawo inda aka zakulo kyawawan nasarorin ta da yadda shugabannin ta na matakin jiha bisa jagorancin Alhaji Idris Yau Mai Unguwa  da kuma na kananan hukumomi suke gudanar da aiyukan su ba tare da nuna son zuciya ba, wanda hakan ta sanya manoman Jihar tafiya da murya daya.

Da yake karbar takardar yabon a ofishin kungiyar dake birnin Dutse, jami’in mulki da hulda da jama’a na kungiyar Malam Mahmoud Hussain Dutse, ya bayyana farin cikin kungiyar bisa damka mata takardar yabo da kafar sadarwa ta Media Action-Nigeria ta yi kan kokarin da ake yi wajen shugabanci.

Sannan ya sanar da cewa takardar tazo daidai lokacin da kungiyar ke Kara cimma nasarori wajen bunkasa hada kan manoma da samar da fahimtar juna tsakanin makiyaya da manoma musamman ganin yadda shugaban kungiyar Alhaji Idris Yau Mai Unguwa yake kokari wajen tabbatar da cewa akwai zaman lafiya tsakanin manoma da yan uwan su makiyaya a fadin jihar Jigawa.

A karshe Mahmoud Hussain Dutse, ya yi godiya ga Gwamnatin jihtar Jigawa a madadin kungiyar ta AFAN saboda kokarin da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ke yi wajen inganta tattalin arziki da zamantakewa ta fannin noma da kuma kiwo, tare da yin godiya ga wannan cibiya ta Media Action-Nigeria.

Leave a Reply