Kotu ta ɗaure matashi ɗan kirifto a Kaduna saboda zamba ta Instagram

0
527

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ɗaure matashi mai harkokin kuɗi ta intanet wato Cryptocurrency tsawon wata uku a gidan yari bayan ta kama shi da laifin zamba.

Mai Shari’a Darius Khobo ya yanke wa Emmanuel Simon hukuncin ne a ranar Alhamis bayan hukuamr EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta gurfanar da shi a gaban kotunsa bisa zargin aikata zamba ta intanet.

An tuhumi Mista Simon da yin amfani da shafin dandalin zumunta na Instagram ɗauke da sunan Hakc4ord da kuma Mrs Gina daga jihar California ta Amurka.

Rahoton shari’ar da EFCC ta wallafa ranar Juma’a ya ce matashin kan tura wa mutane saƙon cewa su zuba jari a harkar kirifto tare da yi musu alƙawarin za su samu riba cikin kwana bakwai.

Leave a Reply