Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu sai baba-ta-gani

0
18
Kotu ta ɗage shari'ar Nnamdi Kanu sai baba-ta-gani

Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu sai baba-ta-gani

A ranar Litinin shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu ya ƙalubalanci hurumin kotu a kan zargin ta’addancin da ake masa lokacin da ya bayyana gaban Mai Shari’a Binta Nyako ta babbar kotun tarayya domin ci gaba da sauraron shari’arsa.

Duk da dagewar da Kanu ya yi a kan cewa Mai Shari’a Nyako ba ta da hurumin sauraron karar, alkaliyar ta dage sauraron har illa masha Allahu.

A watan Yunin 2021 aka dawo da Kanu zuwa Najeriya kuma tun lokacin yake tsare tare da fuskantar shari’a a kan zargin ta’addanci.

KU KUMA KARANTA:A ranakun 19 da 20 ga watan Maris za’a ci gaba da sauraron shari’ar Nnamdi Kanu

Shari’ar ta samu tsaiko bayan da Mai Sharia Nyako ta tsame kanta daga sauraron karar bayan da wanda ake tuhuma ya gabatar da bukatar yin hakan da baki a ranar 24 ga watan Satumban 2024.

Kai tsaye shugaban kungiyar ta IPOB ya shaidawa alkaliyar cewa ya yanke kauna akan yadda take gudanar da shari’ar.

Leave a Reply