Kotu ta yanke wa “Mama Boko Haram” da wasu mutane biyu hukuncin ɗaurin shekaru 10.

0
154

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, shiyyar Maiduguri, ta samu nasara a ƙarar da ta shigar kotu inda aka yanke wa Aisha Alƙali Wakil, wacce aka fi sani da “Mama Boko Haram” da Saidu Daura, da kuma Prince Lawal Shoyode. hukuncin ɗaurin shekaru goma.

Mai shari’a, Umaru Fadawu na babbar kotun jihar Borno ne ya yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru goma Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024.

KU KUMA KARANTA:Matsalar ƙarancin abinci za ta ta’azzara a Sudan saboda fari — MƊD

Lauyan mai gabatar da ƙara, A.I Arogha ya gabatar da shaidu huɗu tare da gabatar da wasu takardu goma sha bakwai a matsayin shaida a gaban kotu yayin sauraron ƙarar da duka ba su wanke waɗanda ake tuhumar ba.

Sakamakon haka, Mai shari’a Fadawu ya yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru goma a gidan yari bisa laifin haɗa baki, sannan ya umarce su da su biya Naira miliyan 40 a matsayin diyyar waɗanda abin ya shafa.

Idan ba a manta ba, an fara gurfanar da waɗanda ake tuhumar ne a ranar 14 ga Satumba, 2020 a gaban Mai shari’a Kumaliya, kan tuhume-tuhume biyu da suka shafi haɗa baki da yaudara wajen karɓar kuɗi har Naira Miliyan Arba’in daga wani kamfani da cewa za su samar masu da waɗansu kayan aiki amma suka danne kuɗin.

Leave a Reply